Da Dumi-Dumi: Kwamishinoni 11 sun yi murabus daga gwamnatin Tambuwal

Da Dumi-Dumi: Kwamishinoni 11 sun yi murabus daga gwamnatin Tambuwal

  • Yayin da ake yaɗa jita-jitar sauya shekar Tambuwal bayan ya gana da Buhari, kwamishinoninsa 11 sun aje aikinsu
  • Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Ɗan'iya, ya sauka da kujerar kwamishinan kananan hukumomi
  • Sauran sun haɗa da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati da sakataren gwamnatin Sokoto

Sokoto - Aƙalla kwamishinoni 11 sun aje aikinsu daga a majalisar gwamnatin jihar Sokoto, karkashin jagorancin gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Daily Trust ta tattaro cewa kwamishinonin sun haɗa da na ma'aikatu kamar; ƙasa da gidaje, Aminu Bala Bodinga; matasa da wasanni, Bashir Gorau; kudi, Abdussamad Dasuki; tsaro, Garba Moyi; harkokin addinai, Abdullahi Maigwandu.

Sauran sun haɗa da kwamishinan ayyuka, Salihu Maidaji; ma'adanan ƙasa, Abubakar Maikudi; albarkatun ruwa, Shu’aibu Gwanda Gobir; da kwamishinan Mahalli, Sagir Bafarawa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari cikin sauki, zai lale miliyan N100m

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Da Dumi-Dumi: Kwamishinoni 11 sun yi murabus daga gwamnatin Tambuwal Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Haka nan kuma mataimakin gwamnan jihar, Manir Dan'iya, ya aje muƙamin kwamishinan kananan hukumomi, sai kuma kwamishinan Kasuwanci, Bashir Gidado.

Bayanai sun nuna cewa Sakataren gwamnatin jihar Sokoto, Sa’idu Umar Ubandoma, da kuma shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Mukhtar Umar Magori, duk sun yi murabus.

Tambuwal ya amince da murabus ɗin su

Rahoto daga gidan gwamnatin Sokoto, ya bayyana cewa gwamna Aminu Tambuwal ya amince da murabus din mutanen.

A cikin mako biyu da suka shuɗe, kusan kwamishinoni 50 ne suka aje ayyukan su a jihohi daban-daban kan babban zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Sashi na 84 (12) na kundin dokokin zaɓe 2022 ya bayyana cewa:

"Babu wani mai rike da muƙami a kowane mataki da zai zama Deleget ko a zaɓe shi a wani taro na kowace jam'iyyar siyasa da nufin tsayar da ɗan takarar zaɓe."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun kashe shugaban tsagin jam'iyyar APC a Bayelsa

A wani labarin kuma Jerin Sunayen gwamnonin APC, PDP da suka shirya janye wa Jonathan takarar shugaban ƙasa a 2023

Wasu fitattun yan siyasa sun shirya canza kudirinsu na neman takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Wasu gwamnoni biyu masu ci sun yanke cewa zasu iya janye wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262