Jerin Sunayen gwamnonin APC, PDP da suka shirya janye wa Jonathan takarar shugaban ƙasa a 2023
- Wasu fitattun yan siyasa sun shirya canza kudirinsu na neman takara a babban zaɓen 2023 dake tafe
- Wasu gwamnoni biyu masu ci sun yanke cewa zasu iya janye wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, takara a 2023
- Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da kuma gwamna Ben Ayade na Kuros Riba sun bayyana dailin da zai sa su janye
Gabanin babban zaɓen 2023, gwamnoni biyu daga APC da PDP sun ce zasu janye aniyarsu ta neman takarar shugaban ƙasa idan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya shiga tseren.
Jita-jita na ƙara yawaita cewa da yuwuwar tsohon shugaban ya zama wanda zai gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a 2023.
Waɗan nan gwamnoni da suka ce zasu janye wa Jonathan sun sanar da cewa za su ɗauki matakin ne saboda, "Nigeria ta cancanci abu mafi kyau."
Sun bayyana haka ne duk da ana yaɗa jita-jitar cewa akwai yuwuwar Jonathan ya sauya sheƙa zuwa APC kuma ya nemi takara a zaɓen 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ya haɗo muku gwamnonin biyu, ga su kamar haka:
1. Bala Muhammed na jahar Bauchi
Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, na ɗaya daga cikin masu hangen kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.
Gwamnan wanda ke cigaba da yawon neman shawari, ya bayyana cewa a shirye yake ya janye takara saboda ganin girman Jonathan.
Muhammed ya yi wannna furucin ne ranar Lahadi da daddare, 24 ga watan Afrilu, yayin da ya bayyana a cikin shirin Channels tv.
Meyasa zai janye wa Jonathan?
Da yake bayyana dalilansa na janye wa Jonthan wanda ya naɗa shi Ministan babban birnin tarayya Abuja a shekarar 2010, Muhammed ya ce:
"Yana daga cikin mutanen da nake ganin ƙimar su fiye da kowa a ƙasar nan. Na fi ganin girmansa kan kowa saboda ta hannunsa tauraruwata ta haska a matakin ƙasa."
"Ta haka na gina alaƙa mai ƙarfi tare da shi, kuma a wajena, ba zai yuwu yana takara kuma nima ina takara ba, babu wannan ƙimar da nake ba shi kenan."
2. Ben Ayade na Kuros Riba
Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya ce zai goyi bayan tsohon shugaban ƙasa Jonathan matuƙar APC ta zaɓi tsayar da shi takara a 2023.
Ayade ya tabbatar da haka ne bayan gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa Aso Villa ranar Talata 26 ga watan Afrilu, 2022.
Ya ce:
"Ina matukar ganin ƙimar shugaba Jonathan, saboda haka ba ni da damuwa kan komai."
A wani labarin kuma Gwamna Ayade ya fallasa kalaman da shugaba Buhari ya gaya masa kafin ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa
Gwamna Ayade na jihar Kuros Riba ya ce shugaban ƙasa Buhari ne ya ba shi shawarar ya fito takara a fafata da shi.
Gwamnan wanda ya gana da Buhari kafin ayyana shiga takara, ya bayyana abinda suka tattauna da shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng