Wasu masoyan shugaba Buhari sun koma bayan Kwankwaso ya gaji shugaban ƙasa a 2023

Wasu masoyan shugaba Buhari sun koma bayan Kwankwaso ya gaji shugaban ƙasa a 2023

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na gaje Buhari a 2023
  • Wata ƙungiyar yan a mutun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta tabbatar da goyon bayanta ga jagoran Kwankwasiyya
  • Ta bukaci jam'iyyar APC ka da ta fitar da ɗan takara a zaɓen 2023, domin da yuwuwar ta sha kunya

Kano - Wata ƙungiyar masoyan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta buƙaci jam'iyyar APC kada ta tsayar da ɗan takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Maimakon haka Ƙungiyar karkashin inuwar ƙungiyar kare muradan Buhari da gamayyar yan takara ta nuna goyon bayanta ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso kana ta shawarci APC ta goya masa baya.

Daily Trust ta rahoto cewa a kwanakin nan, Kwankwaso ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari kuma a ƙarƙashinta ne zai nemi takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Ya kamata Atiku ya janye mun saboda basira ta, Gwamnan Arewa dake mafarkin gaje Buhari

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Wasu masoyan shugaba Buhari sun koma bayan Kwankwaso ya gaji shugaban ƙasa a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Injiniya Miftahu Aliyu Hassan kuma tsohon ɗan takarar kujerar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Mazaɓar Tarauni a zaɓen 2019, shi ne ya bayyana matsayar su ga manema labarai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi ga yan jarida a Legas, Injiniya Aliyu Hassan, ya ce ƙungiyar su, wacce ke da rassa a dukkan jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja, ta cimma matsayar koma wa bayan Kwankwaso.

Ya ce sun amince su yi aiki tare da tsohon gwamnan wajen ganin ya cimma nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe.

APC zata ji kunya idan ta tsayar da ɗan takara

A cewar ɗan siyasan ɗan asalin jihar Kano, jam'iyya mai mulki zata kunyata kanta ne matukar ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe na gaba.

A jawabinsa ya ce:

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi Sallar Jana'izar Alaafin Oba Lamidi Adeyemi

"Jam'iyyar APC da ƙungiyar mu ke ciki ta gaza a muhimman ɓangarori na tsaro, tattalin arziƙi, da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa."

A wani labarin kuma Rikicin APC a Kano, Sanata Shekarau ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC

Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin barin APC.

Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce da su aka yanke wa APC cibiya, yanzun suna dakon hukuncin Kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262