Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

  • Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta gayyaci masu neman takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyu daban-daban zuwa Villa domin su yi buda baki tare
  • Sai dai a wasikar gayyatan, an umurce su da su tawo da katin gayyatarsu kawai sannan su ajiye wayoyinsu a gida
  • Za a yi taron ne da misalin karfe 6:30 da yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, a wani dakin taro na fadar shugaban kasa

Abuja - Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta gayyaci dukkanin yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun siyasa zuwa taron buda bakin Ramadana a fadar shugaban kasa.

Za a gudanar da taron shan ruwan ne a dakin taro na gidan gwamnati a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, da misalin karfe 06:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Kofar rashawa: 'Yan Najeriya sun kadu da jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m a APC

Kada kowa yazo da waya: A'isha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu
Kada kowa yazo da waya: A'isha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu Hoto: Nigeria News
Asali: UGC

A wasikar gayyatan, an umurci yan takarar da kada su zo da wayarsu sai katin gayyatar kawai wanda shine zai basu damar shiga fadar shugaban kasar.

Sai dai kuma, wannan umurnin bai shafi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni da ministocin da ake sanya ran zuwansu taron ba, Punch ta rahoto.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho, kakakin uwargidar shugaban kasar, Aliyu Abdullahi, wanda ya tabbatar da taron ya ce:

“Babu wani abu a nan. Wannan tsari ne na Villa idan kana da ganawa da daya daga cikin mazauna fadar shugaban kasa.
“Idan za su zo wani taro, wannan abu ne da ya kamata DSS su tilasta shi a lokacin da shugaban kasa ke wani taro ko mataimakin shugaban kasa na da wani taro ko uwargidar shugaban kasa na da wani taro. Saboda yan waje za su zo. Wannan shine tsaron da tsarin.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu

“Hakan bai shafi mataimakin shugaban kasa ba. Ta yaya za ka yi tsammanin hakan zai shafi mataimakin shugaban kasa koma ministoci?”

Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi 36 zuwa taron buda baki a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu.

Har ila yau, daga cikin wadanda shugaban kasar ya gayyata taron buda bakin harda manyan hafsoshin tsaro na kasar da wasu manyan jami'an gwamnati.

Wasu daga cikin mutanen da aka gayyata sun yi sallar Magrib tare da shugaban kasar a masallacin fadar shugaban kasa kafin aka fara taron buda bakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng