Jagororin APC 20 da suka sa baki aka yi wa ‘Yan kasa da shekara 40 rangwamen fam
- Shugaban matasan APC na kasa ya bada sanarwar cewa za ayi wa duk wani matashi rangwamen sayen fam din shiga takara a jam’iyyar mai mulki
- Dayo Israel ya bayyana wannan nasara da aka samu a shafinsa na Twitter a ranar Laraba. Hakan na zuwa ne bayan taron NEC da aka gudanar a Abuja
- Kamar yadda Dayo Israel ya fada, duk wanda bai kai shekara 40 ba, zai saye fam din ne a rabin farashin da za a saidawa sauran masu neman shiga takara
The Cable ta ce sabon shugaban matasan na jam’iyyar APC mai mulki ya yi kira ga mutane cewa su yi amfani da wannan dama da ba a taba samun irin ta ba.
Hakan na nufin matasan da ke neman takarar gwamna za su biya N25m a maimakon N50m. Masu harin kujerar majalisar wakilan tarayya za su kashe N5m.
Sannan kuma ‘yan kasa da shekara 40 za su saye fam din takarar majalisar dokoki a kan N1m. Mai neman zama Sanata a zaben 2023 zai saye fam a kan N10m.
Legit.ng Hausa ta fahimci Israel da mataimakinsa kadai ne masu kananan shekaru da suka halarci taron majalisar kolin na jam’iyyar APC mai mulki a Abuja.
Wadanda suka yi kokari
Israel ya ambaci duk wadanda suka taimaka wajen ganin an yi wa matasa wannan rangwame a taron da aka gudanar. Ga su nan kamar yadda ya jero su a Twitter:
1. Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila
2. Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
3. Gwamnan jihar Legas, Jide Sanwo-Olu
4. Gwamna jihar Kogi, Yahaya Bello
5. Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma
Sauran wadanda suka taka rawar gani sun hada da
6. Shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu
7. Sakataren jam’iyya, Iyiola Omisore
8. Gwamna Simon Lalong
9. Gwamna Rotimi Akeredolu
10. Gwamna Badaru Abubakar
11. Gwamna Gboyega Oyetola
12. Gwamna Aminu Masari
13. Gwamna Bello Matawalle
14. Gwamna Kayode Fayemi
15. Mataimakin Gwamnan jihar Enugu
16. Mataimakin Gwamnan jihar Kano
Sai kuma
17. Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Ahmed Wase
18. Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo Agege
19. Mataimakin shugaban kasa da
20. Mai girma shugaban kasa
Matasa za su amfana
Da farko, Muttaqa Abdul Hadi Dabo wanda yake da niyyar fitowa takarar gwamnan Kaduna ya yi mamakin jin yadda jam’iyyar APC ta lafta kudin fam a N50m.
Sardaunan a bari ya huce ya ce zai bunkasa ilmi, samar da aikin yi, yaki talauci, inganta harkar noma da samar da ruwan sha idan ya zama Gwamnan Kaduna.
Shi kuma hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad mai neman yin takarar kujerar ‘dan majalisar tarayya a APC ya bada shela a Facebook cewa zai je sayen fam.
Ahmaad mai shekara 31 yana cikin wadanda za su ci moriyar wannan sauki da aka yi wa matasa. Zai nemi kujerar Gaya/Albasu/Ajingi a majalisar wakilai a APC.
Asali: Legit.ng