Abinda ya hana Bola Tinubu halartan taron NEC na jam'iyyar APC, Rahman

Abinda ya hana Bola Tinubu halartan taron NEC na jam'iyyar APC, Rahman

  • Hadimin jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta bangaren midiya, Tunde Rahman ya faɗi dalilin rashin zuwan Tinubu taron NEC
  • Ya bayyana cewa ɗan takaran shugaban ƙasa ba shi daga cikin mambobin majalisar NEC shiyasa ba'a ga kafarsa ba
  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Osinbajo da shugaban APC na ƙasa duk sun halarci wurin yau Laraba

Lagos - Hadimin jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ta ɓangaren midiya, Tunde Rahman, ya bayyana dalilin rashin ganin ɗan takarar shugaban ƙasan a wurin taron majalisar ƙoli (NEC) na APC.

Hadimin Tinubun, ya kare uban gidansa ne a wata tattauna wa da wakilim jaridar Punch ranar Laraba.

A ranar Laraba, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ta gudanar da taron majalisar koli domin tattauna batutuwa masu muhimmanci game da shirin tunkarar zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya kaɗu da jin kuɗin fam Miliyan N100m

Jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu.
Abinda ya hana Bola Tinubu halartan taron NEC na jam'iyyar APC, Rahman Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/facebook
Asali: Facebook

Tun da farko dai, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya halarci wurin taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya je taron da mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da kuma shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Sauran waɗan da suka halarci taron sun haɗa da sauran yan kwamitin gudanarwa (NWC) da Sanata Adamu ke jagoranta, mambobin kwamitin amintattu da gwamnonin APC.

Meyasa Bola Tinubu bai halarci wurin ba?

Rahman ya ce kundin tsarin mulkin APC bai ba Bola Tinubu damar zuwa wurin taron ba kasancewar ba ya cikin majalisar NEC.

Ya ce:

"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba mamba bane a majalisar NEC, shi ɗan majalisar mambobin APC ne. Mambobin NEC sun haɗa da shugaban ƙasa, mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa."
"Sai kuma kakakin majalisar wakilai, shugabannin APC na jihohi da kuma mambobin kwamitin gudanarwa (NWC)."

Kara karanta wannan

Ngige ya ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2023, ya faɗi wasu kalamai kan Buhari da APC

A wani labarin kuma Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilaisa na ɗaukar matakin

A yan kwanakin nan jam'iyyar APC na cigaba da samun koma baya duba da yadda wasu jiga-jiganta ke sauya sheka a wasu sassan ƙasar nan.

A yau Talata, tsohon Ministan Buhari, Solomon Dalung, ya mika takardar ficewa daga jam'iyya ga mahukuntan APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262