Tsohon Gwamna kuma Aminin Buhari ya shirya tsaf domin takarar Shugaban kasa a APC

Tsohon Gwamna kuma Aminin Buhari ya shirya tsaf domin takarar Shugaban kasa a APC

  • Sanata Ibikunle Amosun yana daf da bada sanarwar cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023
  • Sanata mai wakiltar mazabar Ogun ta tsakiya a majalisar dattawa zai nemi tikitin jam’iyya mai mulki
  • Ibikunle Amosun yana tare da Muhammadu Buhari tun a Jam’iyyar ANPP a 2003, kafin kafa APC

Ogun - Ibikunle Amosun wanda yanzu haka shi ne Sanata mai wakiltar mazabar Ogun ta tsakiya a majalisar dattawa zai jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa.

Jaridar The Cable ta ce Sanata Ibikunle Amosun ya shirya domin bayyana shirin fitowa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa tsohon gwamnan na Ogun zai fadawa Duniya wannan kudiri ne a wajen taro da za a kira a farkon watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Shugaban Kasa ya koma gida, zai shiga takarar ‘Dan Majalisa a Kano

“An kammala komai. Zai kaddamar da niyyar takara a ranar 5 ga watan Mayu.” - Majiya.

Idan labarin ya tabbata, Ibikunle Amosun zai kalubalanci Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Rochas Okorocha da Rotimi Amaechi wajen samun tikitin APC.

The Tribune ta karfafi wannan rahoto, ta ce Sanatan na Ogun yana shawara da mutane a kan wannan batu. Zai kaddamar da shirin takara ne a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Gwamnan Osun a fadar Shugaban kasa a APC
Akinlade, Buhari da Amosun a fadar Shugaban kasa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sauran wadanda suke sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a 2023 sun hada da David Umahi, Yahaya Bello da Sanata Orji Uzor Kalu.

Zamansa a jam’iyyar ANPP

Amosun na hannun dama ne a wajen shugaban kasa tun ba yau ba. Sannan kuma yana cikin ‘yan APC a Kudu maso yamma da ba su tare da Tinubu a yau.

Sanata Amosun ya yi takarar gwamna a ANPP a 2003 amma bai yi nasara ba. Kafin zamansa gwamna a ACN, ya yi shekaru hudu a majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso na shirin bayyana aniyarsa ta danewa kujerar Buhari

Zargin yi wa APC zagon-kasa

Maganar takarar Sanatan na zuwa ne shekaru uku bayan an yi rigima a game da zaben gwamnan da zai gaje shi, har ta kai ya goyi bayan jam’iyyar APM.

A lokacin yana shirin barin mulki, Amosun ya so Adekunle Akinlade ya samu tikitin APC, da bai yi nasara ba, sai ya mara masa baya a karkashin APC.

A dalilin wannan ne uwar jam’iyya ta dakatar da shi bayan zaben 2019 na wani tsawon lokaci. Daga baya kuma sai aka ji an janye wannan dakatarwa.

Tinubu zai yi takara

A makon da ya wuce aka rahoto cewa Asiwaju Bola Tinubu ya kaddamar da yakin neman zabensa ga matasan jam’iyyar APC a wani taro a Legas.

‘Dan siyasar ya soki shugabannin da aka yi, ya yi ikirarin duk sun gasa cika alkawuran da suka yi. Tinubu ya yi wata magana da kamar suka ce ga Buhari.

Kara karanta wannan

Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel