Da Dumi-Dumi: Sanata Mai Wakiltar Mazabar Shugaba Buhari ya fice daga APC, ya koma PDP
- Sanata Ahmad Babba Kaita mai wakiltar Katsina ta arewa a Majalisar dattawa ta kasa ya fice daga APC ya koma PDP
- Rahoto ya nuna cewa Kaita ya miƙa takardar murabus daga APC a gundumarsa dake yankin karamar hukumar Kankiya ranar Talata
- Wannan dai na zuwa ne bayan alaka ta yi tsami tsakanin sanatan da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari
Katsina - Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Katsina ta arewa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Babba Kaita ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.
Katsina ta arewa wacce ta kunshi yankin Daura da kewayenta, nan ne yankin mazaɓar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Aminiya ta rahoto.
Bayanai sun nuna cewa Sanata Babba Kaita ya miƙa takardar murabus daga APC a gundumarsa dake ƙaramar hukumar Kankiya ta jihar Katsina ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, 2022.
Meyasa Sanatan ya ɗauki matakin barin APC?
Mutane na gani matakin ficewa daga APC da Sanata Babba Kaita ya ɗauka ba zai rasa alaƙa da rashin jituwar dake tsakaninsa da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ba.
Babba Kaita ya jima yana sukar lamirin gwamnatin Katsina, musamman kan ƙin gudanar da zaɓen kananan hukumomi tun bayan kafa gwamnatin a 2015.
Sai dai a yan kwanakin nan a cikin wannan watan na Afrilu, aka gudanar da zaɓen kannan hukumomi a faɗin jihar Katsina, wanda hukumar zaɓe ta ce APC ta lashe dukkan kujeru.
A wani labarin kuma Daga Karshe, Minista Ngige ya ayyana shiga takarar shugaban kasa, ya faɗi wasu kalmomi
Bayan dogon lokaci ana yaɗa jita-jita, Ministan Kwadugo da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari.
Dakta Ngige, wanda ya yaba wa gwamnatin APC, ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai ba mutane kunya ba.
Asali: Legit.ng