Gwamnan APC ya na goyon bayan Mai dakinsa tayi takarar Sanata a wata Jihar dabam
- Gwamnan jihar Ondo ya fitar da jawabi da ya yi wa taken ‘Public Service: The Greatest Privilege’
- Oluwarotimi Akeredolu ya bayyana goyon bayan shi ga mai dakinsa, Mrs. Betty Anyawu a zaben 2023
- Uwargidar gwamnan Ondo ta na so ta yi takarar kujerar Majalisar Dattawa a inda ta fito, gabashin Imo
Ondo - Mai girma gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya fito yana goyon bayan takarar mai dakinsa, Betty Anyawu a zabe mai zuwa na 2023.
Daily Trust ta ce Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya fitar da jawabi, ya bayyana cewa yana goyon bayan Betty Anyawu ta nemi kujerar Sanata a jihar Imo.
Madam Betty Anyawu ta na da shirin shiga zabe, inda za ta yi takarar zama ‘Yar majalisa mai wakiltar mazabar gabashin jihar Imo a majalisar dattawa.
A jawabin da Gwamnan ya fitar a ranar Litinin, ya ce takarar Anyawu zai cire mata daga kangi da duk wani nau’i na hana su cigaba da ake yi a kasar nan.
Rotimi Akeredolu ya yabi uwargidar jihar Ondo da cewa mata ce mai ‘yanci da kokarin cin gashin kan ta, wanda ba ta tsoron ta fito ta tofa albarkacin bakinta.
Shekaru 41 da yin aure
Rahoton ya ce gwamnan ya zabi ya ba takarar uwargidarsa goyon baya ne a ranar da suke bikin cika shekaru 41 da yin aure, tun 1981 yake tare da matarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda gwamnan yake fada, ana samun cigaba a Duniyar yau ne a lokacin da aka samu wasu tsirarrun mutane da suka ciri tuta a cikin al’ummarsu.
Akeredolu ya ce masu kokarin canza yadda abubuwa suke tafiya, su kan yi tasiri a rayuwar jama’a.
“Bari in yi amfani da wannan muhimmiyar rana, da mu ke cika shekara 41 da aure, in nunawa Duniya goyon bayan da na ke yi maki a burinki na yi wa mutanenki hidima.”
- Rotimi Akeredolu SAN
Za a gwabza a yankin Owerri
Legit.ng Hausa ba ta da labarin a jam’iyyar da Betty Anyawu za ta tsaya takara. Mai gidanta bai bayyana wannan a jawabin da ya fitar daga garin Akure ba.
Babu mamaki Anyawu mai shekara 68 za ta kara da Sanata mai-ci, Ezenwa Francis Onyewuchi wanda yake jam’iyyar PDP idan har ya sake samun tikitin PDP.
Tinubu a zaben 2023
Kun ji cewa babban ‘dan siyasar nan na kudancin Najeriya, Bola Tinubu ya na cikin wadanda suke da goyon bayan ‘yan jam’iyya a zaben shugaban kasa.
Akwai wasu tsofaffin Sanatoci, Ministoci ‘Yan Majalisa, Gwamnoni, da Sojoji da sun dage da gaske a game da samun takarar Tinubu a karkashin jam'iyyar APC/
'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Kwana 4 Bayan Sanar Da Takararsa
Asali: Legit.ng