Ka cire rigar Malunta ka shigo siyasa, Fadar shugaban kasa ta yiwa Bishop Kukah raddi

Ka cire rigar Malunta ka shigo siyasa, Fadar shugaban kasa ta yiwa Bishop Kukah raddi

  • Malam Garba Shehu ya zazzage fushi kan Babban Limamin Katolikan Sakkwato, Matthew Kukah
  • Mai magana da yawun Buharin yace Bisho Kukah ya cire rigar Malunta ya shiga siyasa idan zai kai labari
  • Matthew Kukah, a ranar Lahadi, ya yi kakkausar suka ga Buhari kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa

Abuja - Fadar shugaban kasa a ranar Litinin ta mayar da martani ga Bishop Mattew Hassan Kukah, bisa caccakar Shugaba Muhammadu Buhari da yayi a sakonsa na barka da Easter.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a jawabin da ya fitar ya yi kira da Bishop Kukah ya cire rigar Malunta ya shiga siyasa ya gani ko zai kai labari.

Kara karanta wannan

Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargitsa kasar nan

Garba Shehu yace tuni dama Bishop Kukah ya ki jinin shugaba Buhari.

Yace:

"Yan Najeriya tuni sun san ra'ayoyin Bishop Kukah kan gwamnatin nan. Ya bayyana karara cewa bai son gwamnatin nan tun ranar da aka zabeta."
"Amma ya sani cewa yan Najeriya sun zabi gwamnatin nan sau biyu. Basu yaudaru da kalaman kin jininsa ba."
"Muna kira ga Bishop Kukah ya mayar da hankali kan harkar maluntarsa ya bar mutane da yan siyasa kamar yadda ya bayyana a littafin Bible James 1:27."
"Idan ba haka ba, ya cire rigar Malunta ya shiga siyasa ya gani ko zai kai labari."

Bishop Kukah raddi
Ka cire rigar Malunta ka shigo siyasa, Fadar shugaban kasa ta yiwa Bishop Kukah raddi
Asali: UGC

Zaku tun cewa Babban Limamin Katolikan, Matthew Kukah, a ranar Lahadi, ya yi kakkausar suka ga Buhari kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da rarrabuwar kawuna a Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Ubangiji Ya Min Wahayi, Zan Ƙaddamar Da Takarar Shugaban Ƙasa Ta Ranar Talata, Ministan Buhari

Kukah ya bayyana kokensa a cikin sakonsa na Ista mai taken, ‘To mend a broken nation: The Easter metaphor’.

A cewar Bishop din, 'yan siyasa sun lalata kowane fanni na rayuwa a Najeriya yayin da suke cin hanci da rashawa.

Femi Adesina ne ya fara martani

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya wanke mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sukar da ake masa na cewa salon mulkinsa ya raba kan 'yan Najeriya.

Adesina yace abin mamaki ne a ce wadanda suke da laifin haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya su ne ke zargin shugaban kasar da irin laifin da suka aikata.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Adesina ya rubuta cewa:

“Wadanda suka raba Najeriya da bakunansu, da muggan maganganu, magana babu birki, su ne wai yanzu suke tuhumar Shugaba Buhari. Abin bakin ciki! Mugun nufinsu ba zai cika ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel