2023: Ƙungiyar Magoya Bayan Atiku Ta Juya Masa Baya, Ta Rungumi Ɗan Takarar Wata Jam'iyyar Daban

2023: Ƙungiyar Magoya Bayan Atiku Ta Juya Masa Baya, Ta Rungumi Ɗan Takarar Wata Jam'iyyar Daban

  • Wata kungiya ta masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, dan takarar PDP, ta dawo daga rakiyarsa
  • Kungiyar mai suna "Atiku State of Mind" ta ce ta gane kuskurenta na dage wa sai ta goyi bayan yan takara daga manyan jam'iyyun Najeriya biyu
  • A yanzu, kungiyar ta sauya alkibla ta koma goyon bayan Kingsley Moghalu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC)

Kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar mai suna "Atiku State of Mind" ta janye goyon bayanta ga dan takarar na shugaban kasa a PDP ta koma goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Mr Kingsley Moghalu.

The Nation ta rahoto cewa Mr Hassan Ankuma, tsohon shugaban kungiyar na kasa, ne ya bayyana haka a ranar Juma'a, yayin taron manema labarai da ya kira don goyon bayan dan takarar na ADC.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Lokacin Da Zai Ƙaddamar Da Takararsa Na Shugabancin Ƙasa

Ankuma ya ce kungiyar ta yi kurakurai a baya ta hanyar goyon bayan yan takara daga manyan jam'iyyu biyu da ke Najeriya kadai.

2023: Ƙungiyar Magoya Bayan Atiku Ta Juya Masa Baya, Ta Rungumi Ɗan Takarar Jam'iyyar ADC
2023: Ƙungiyar Magoya Bayan Atiku Ta Juya Masa Baya, Ta Rungumi Moghalu. Hoto: Kashope Faje/The Nation.
Asali: Twitter

Ba za mu sake maimaita kura-kuren da muka yi a baya ba, Ankuma

The Herald ta rahoto cewa ya ce kungiyar ba za ta sake maimaita wannan kuskuren ba gabanin babban zaben shekarar 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kuskuren da muka yi a baya shine yan takara daga manyan jam'iyyun siyasa biyu na kasar nan muke goyon baya tamkar su kadai ne yan takara.

Dogaro kan wadannan manyan jam'iyyun biyu ne yasa muka rika zaben shugabanni marasa nagarta su kadai muke zaba ko da wadanda suka tsayar ba su da nagarta.

Yanzu mun gane cewa Najeriya na kara lalacewa kuma muna fargabar abin da zai faru a nan gaba hakan yasa muka yi nazari muka sauya tsari.

Kara karanta wannan

Sakataren Gwamnati Ya Yi Murabus Daga Kan Muƙaminsa, Ya Shiga Tseren Takara a 2023

"A yau, muna da mambobi daga Rivers zuwa Borno da Sokoto da Nnewi domin fara sabuwar tafiya bisa sabon bayani da muka samu.
"Ni da tawaga ta mun sauya daga kungiya ta goyon bayan Atiku mai suna "Atiku State of Mind" zuwa "Moghalu State of Mind".
"Muna son kasa mai inganci da zaman lafiya wacce za ta tabbatar an cika wa mutane alkawurran da aka dauka yayin yakin neman zabe.
"Ba mu son shugaba da zai rika tunanin kasaitarsa ce ta sa aka zabe," in ji Ankuma.

Moghalu ya bayyana abin da zai yi don habbaka tattalin arzikin Najeriya idan an zabe shi

Ya yi kira ga yan Najeriya su goyi bayan jam'iyyar ADC kuma ya roki jam'iyyar ta bawa Moghalu tikitin takara don tabbatar da adalci ga yankin kudu maso gabas.

A jawabinsa, Mr Moghalu, dan takarar shugaban kasa na ADC ya yi alkawarin zai habbaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar rage dogaro kan fetur idan an zabe shi a 2023.

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164