2023: Kwankwaso Ya Bayyana Lokacin Da Zai Ƙaddamar Da Takararsa Na Shugabancin Ƙasa
- Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zai kaddamar da takararsa cikin mako mai zuwa
- Kwankwaso ya ce ya dauki lokaci yana tuntubar abokansa da sauran al'umma da masu ruwa da tsaki kuma ya samu goyon bayansu
- Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce babban zaben shekarar 2023 za a fafata ne tsakanin masu son canji da masu son kasar ta cigaba da zama yadda ta ke
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirye-shiryen kaddamar da takararsa na shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Daily Nigerian ta rahoto.
Da ya ke magana yayin taron manema labarai a ranar Juma'a, Kwankwaso ya ce ya tuntubi mutane da dama kuma sun bashi goyon baya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na tuntubi abokai na da yan Najeriya daga bangarori da dama kuma na samu goyon baya. Zan sanar da yan Najeriya takara ta mako mai zuwa," in ji shi.
News Digest ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya nuna gamsuwarsa bisa goyon bayan da NNPP ke samu duba da yadda mutane ke rajista a jam'iyyar.
Ya kara da cewa zaben 2023 za a fafata ne tsakanin wadanda ke son canji da wadanda ke son lamura su cigaba a yadda suke a yanzu.
Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta zage damtse don ganin ta samar da tsaro a kasar
Kwankwaso ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kara dagewa wurin magance rashin tsaro, yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta karfafa wa hukumomin tsaro gwiwa su kawar da yan ta'adda.
Ya ce a matsayinsa na tsohon ministan tsaro, bai taba tsammanin tsaro zai tabarbare haka ba.
Kwankwason ya ce ya kamata shugabannin kasar su mayar da hankali wurin horas da sojoji da basu makamai wadanda suka fi na yan ta'addan.
Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP
A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.
An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.
‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.
Asali: Legit.ng