2023: Kwankwaso na hararo kujerar Buhari, ya ce tazarcensa ba ta amfani Najeriya da komai ba
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tazarcen shugaba Buhari ba ta amfani 'yan Najeriya da komai ba face bacin lokaci
- Tsohon gwamnan Kanon kuma tsohon ministan tsaron, ya ce bai taba tsammanin rashin tsaro zai yi kamari a kasar nan cikin shekaru kadan ba
- Ya jaddada cewa, jam'iyyar NNPP za ta zo kuma za ta ceci mutanan kasar nan daga mummunan halin rashin tsaro da suke ciki
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu a matsayin wata damar da ya bata na cika alkawarin da ya yi ga ‘yan Najeriya.
Ya ce gwamnatin da za ta kammala aikinta cikin 'yan watanni, ba ta magance wasu batutuwan da ‘yan kasar ke sa ran shugaba Buhari zai magance ba, Vanguard ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano ne kuma tsohon ministan tsaro, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
A cewarsa, ‘yan Najeriya sun samu kwanciyar hankali a lokacin da suka zabi ‘Canji’ a shekarar 2015 bayan shafe sama da shekaru hudu ana fuskantar tashe-tashen hankula da sauran matsalolin tsaro a kasar.
Sai dai kuma mai fatan zama shugaban kasar ya ce ‘yan Najeriya sun sha mamaki da wannan gwamnati saboda rashin tsaro, a cewarsa ya kara ta’azzara kuma matsalar tattalin arziki ta ta’azzara.
Ya ce, “Da zarar ka kafa gwamnati ko dai a matsayin shugaban kasa ko gwamna, to ka zama na jiha ko kasa baki daya. Kowa naka ne. Kuna da alhakin kare su da tabbatar da cewa mutane sun sami rayuwa mai kyau. Wadannan su ne batutuwa. Da zarar kun rasa duk waɗannan matakan, rashin tsaro zai zama sakamakon”.
A jawabinsa, ya kara da cewa:
"Sun sami damar yin aiki ga kasar, amma ba za su iya ba. Zabe ya kusa karatowa kuma sun yi alkawarin za su yi iya kokarinsu ga Najeriya. Ba mu ga komai ba.
“Kowane soja namiji da mace, ciki har da mutane irina da suka samu damar cudanya da sojoji da sauran jami’an tsaro, dole ne su damu matuka, amma a lokaci guda suna mamakin abubuwan da ke faruwa a kasar nan.
“Abin da muke gani yana faruwa yana da bada takaici. Mutane ba sa maganar yadda za a kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su bayan harin jirgin kasan Kaduna.
“Ya aka yi muka isa nan? Yakamata gwamnati ta kara dagewa a kan tsaro. A matsayina na tsohon Ministan Tsaro, ban taba tunanin rashin tsaro zai taba yin kamari a kasar nan cikin kankanin lokaci ba. Ta yaya muka samu kanmu a cikin wannan kunci? Me ya faru a zahiri?"
Daily Trust ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya ce shugabancin siyasa na yanzu bashi da karfin da ya isa ya zaburar da sojoji da kuma tabbatar da an ba su abin da suke bukata na horo da kayan aiki da makamai da harsasai.
Yayin da yake cewa jam’iyyar APC ta kasa samar da shugabanci da shugabanci nagari ga ‘yan Najeriya, ya ce NNPP za ta karbi ragamar shugabancin kasar nan a shekarar 2023.
Asali: Legit.ng