Tinubu ya tara duk shugabannnin Majalisan APC, sun yarda su mara masa baya a 2023
- Asiwaju Bola Tinubu ya yi zama da shugabannin majalisun jihohi da ke karkashin jam’iyyar APC
- Jagoran na APC ya hadu da tsofaffin shugabannin majalisar dokoki da mataimakan shugabanni
- Tinubu ya na neman goyon bayan ‘ya ‘yan APC, kuma sun yi masa alkawarin za su mara masa baya
Lagos - Shugabannin majalisun dokoki na jihohin kasar nan da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun yi zama da Asiwaju Bola Tinubu a garin Legas.
The Cable ta ce Bola Tinubu ya yi wannan taro ne a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu 2022 domin samun goyon bayan ‘yan majalisar a zaben fitar da gwani.
Asiwaju Bola Tinubu yana cigaba da kokarin tattaunawa da manyan ‘yan siyasa domin ya zama ‘dan takarar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC.
A wani jawabi da Hadimin gwamnan Legas, Gboyega Akosile ya fitar, ya bayyana cewa shugabannin majalisar sun yi alkawarin marawa Tinubu baya.
Rt. Hon. Abubakar Sulaiman wanda shi ne shugaban kungiyar shugabannin majalisar dokoki kuma shugaban majalisar jihar Bauchi, ya karba kiran jigon.
Da yake jawabi a madadin takawarorinsa, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman ya yaba da halin Tinubu, ya kuma tabbatar masa cewa babu shakka za su taya shi yaki.
“Mun san da burinka na zama shugaban kasar nan. Ina mai ba ka tabbacin ‘yan majalisar dokoki a shirye suke da su taya ka cin ma burin nan.”
“Mu na tare da kai a wannan tafiya, saboda haka ka gabatar mana da rokonka na neman mu zama cikin wannan tafiya.” - Hon. Abubakar Sulaiman.
Da yake jawabi a shafinsa na Facebook, tsohon gwamnan na Legas ya tabbatar da wannan zama da aka yi a Ikeja domin samun goyon bayan ‘yan jam’iyyarsa.
A wani bidiyo, an ji ‘dan siyasar yana mai cewa shi ne mutumin da Najeriya ta ke bukata a yanzu.
A cewar ‘dan siyasar, shi ma ya taba zama ‘dan majalisa kamarsu, kuma burinsa ya karbi mulki ta yadda zai tsare Najeriya, ya kawowa mutanen kasar cigaba.
Umahi ba zai fasa takara ba
An ji labari Gwamna David Umahi wanda ya na cikin masu takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya musanya rade-radin hakura da neman tikiti a 2023.
Hadimin gwamnan, Francis Nwaze ya ce babu gaskiya a rahotannin da ke yawo na janye takarar da ya sa gaba, wai zai nemi kujerar Sanatan Ebonyi ta Kudu.
Asali: Legit.ng