Yanzu-yanzu: Shugaban cibiyar lissafi da bahasin gwamnatin tarayya ya mutu, bayan wata 7 da nadashi

Yanzu-yanzu: Shugaban cibiyar lissafi da bahasin gwamnatin tarayya ya mutu, bayan wata 7 da nadashi

  • Najeriya ta yi rashin babban jami'in gwamnati kuma Shugaban cibiyar lissafi, bahasi, da kididdiga
  • Dakta Simon ya mutu ne bayan watanni bakwai da adanmewarsa kan kujerar
  • Masanin ilmin lissafin ya kwashe shekaru talatin a ma'aikatar yana aiki har ya zama shugaba

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa shugaban cibiyar lissafi da bahasi na tarayyar Najeriya NBS, Dr Simon Harry, ya rigamu gidan gaskiya.

Ya mutu ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

An samu jita-jitan mutuwarsa ranar Asabar, karshen makon da ya gabata amma diraktan yada labarai da hulda da jama'a cibiyar NBS, Sunday Ichedi, ya karyata rahotannin.

Amma da safiyar yau Laraba, ya tabbatar da cewa lallai yanzu ya mutu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Simon Harry ne a Agustan 2021 don maye Yemi Kale matsayin shugaban NBS.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari Ya Shiga Jerin Masu Takarar Gwamna a Jiharsa

Ga Abubuwa biyar da ya kamata ka sani game da marigayin:

1. Dan asalin jihar Flato ne, Arewa maso tsakiyar Najeriya

2. Shugaba Buhari ya nada shi shugaban mai kididdigan Najeriya a Agustan 2021

3. Ya shiga aiki cibiyar NBS a shekarar 1992 kuma ya cigaba da aiki har ya zama dirakta a 2019

4. Gabanin zama shugaban cibiyar, ya kasance diraktan shirye-shirye na cibiyar

5. Ya kwashe kimanin shekaru 30 yana aikin gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel