Atiku, Saraki da Tambuwal sai sun dage, ‘Yan takarar Kudu sun hada-kan su a PDP

Atiku, Saraki da Tambuwal sai sun dage, ‘Yan takarar Kudu sun hada-kan su a PDP

  • ‘Yan siyasar kudu maso gabas da ke neman yin takarar shugaban kasa a PDP sun yi zama a Abuja
  • Makasudin zaman shi ne ‘yan siyasar su hada-kai saboda su tsaida ‘dan takara daya daga cikinsu
  • Anyim Pius Anyim, Peter Obi, da Mazi Sam Ohuabunwa su na cikin wadanda aka yi taron nan da su

Abuja - Masu harin kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP daga kudu maso gabashin Najeriya sun yi wani zama a ranar Asabar.

Jaridar Punch ta ce wadanda suka halarci wannan taron sun hada da Anyim Pius Anyim, Peter Obi, Mazi Sam Ohuabunwa da Dr Nwachukwu Anakwenze.

Jiga-jigan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP su na neman a ba yankinsu takara a zabe mai zuwa. A cewarsu, sun bada gudumuwa a lokacin da Arewa ke samun tikitin.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Sanata Anyim Pius Anyim shi ne ya karanto bukatar abokan takararsa, ya ce sun amince za su yi aiki tare domin ganin mutumin Ibo ne aka ba tikitin jam’iyya.

Jawabin Anyim Pius Anyim

“Mun amince mu yi aiki tare da juna domin ganin cewa wanda zai rikewa jam’iyyar PDP ya fito ne daga bangaren kudu maso gabas.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Za mu tattauna da sauran yankuna a kan wannan maganar, domin a samu adalci da daidaito.”
'Ya 'yan PDP
Anyim Pius Anyim, Peter Obi, Mazi Sam Ohuabunwa da Dr Nwachukwu Anakwenze Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“A wajen yin wannan, ya na da muhimmanci a san da mun taimakawa sauran yankuna, kuma mu na so su maida alherin da muka yi.”

- Anyim Pius Anyim

Blueprint ta rahoto Anyim ya na cewa ‘yan jarida za su yi kokarin fito da ‘dan takara guda daga cikinsu ta yadda kowa zai mara masa baya a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

PDP ta na fuskantar barazana a jihohin Kudu idan ta ba Atiku, Saraki ko Tambuwal takara

Ina matsayar gwamnonin Ibo?

Manema labarai sun nemi jin ko wannan ne matsayar gwamnonin Ibo, amma tsohon shugaban majalisar dattawan kasar bai ci masu albasa da bakinsa ba.

Anyim Pius Anyim ya na fatan sauran wadanda za su saye fam din neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP za su shigo cikin wannan tafiyar.

Wike da Obi sun gamu da suka

A makon nan aka ji labari cewa Mujaheed Dokubo-Asari ya na ganin sam Gwamna Nyesom Wike bai dace ya rike Najeriya, bai yi kama da shugaban kasa ba.

Alhaji Mujaheed Dokubo-Asari ya kuma caccaki Peter Obi, ya ce bai yi komai da yake gwamna a jihar Anambra ba. Dukkaninsu su na neman takara a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel