Tazarcen Gwamnan APC ya na lilo a iska, sai yadda ‘Yaran Tinubu’ su ka yi da shi a 2023

Tazarcen Gwamnan APC ya na lilo a iska, sai yadda ‘Yaran Tinubu’ su ka yi da shi a 2023

  • Maganar tazarcen Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta na kasa-ta na dabo a jam’iyyar APC mai mulki
  • Majalisar Governor’s Advisory Council (GAC) ba tayi zama game da takarar Babajide Sanwo-Olu ba
  • A siyasar APC a jihar Legas, idan ‘Yan GAC ba su tare da mutum, zai yi wahala ya iya kai labari a zabe

Lagos – Har zuwa yanzu, babu tabbacin cewa jam’iyyar APC ta reshen jihar Legas, ta na tare da Mai girma Babajide Sanwo-Olu a zabe mai zuwa na 2023.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar Talatar nan ya nuna cewa gaskiya magana ita ce har yau Gwamna Babajide Sanwo-Olu bai san matsayarsa ba.

Rade-radin da ake yi cewa majalisar Governor’s Advisory Council (GAC) ta ba Gwamna mai-ci dama ya zarce a karkashin jam’iyyar APC, ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

APC ta soki Osinbajo don zai yi takara da Tinubu, ta ce bai tsinana komai ba a shekara 7

Wannan majalisa ta mashawarta da ake kira GAC, ita ce koli wajen yanke duk wata shawara a jam’iyyar APC a Legas, ana zargin mutanen Bola Tinubu ne.

Ganin GAC ba ta nuna masa ta na tare da shi ba, shiyasa Gwamnan bai bayyana niyyar tazarce ba. Idan ya yi riga-malam masallaci, zai iya shan mamaki a zabe.

Jaridar ta ce har zuwa yau, ‘Yan GAC ba su yi zama a kan batun tazarcen Gwamna Sanwo-Olu ba.

Gwamnan Legas
Babajide Sanwo-Olu ba da Bola Tinubu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Za a sake yin irin na Ambode?

Haka aka yi da tsohon gwamna Akinwumi Ambode, majalisar GAC ta ki mara masa baya a zaben 2019. A karshe Gwamnan ya na gani ya rasa tikitin jam’iyya.

Wani rahoto da Sahara Reporters ta fitar ya ce akwai jita-jitar jam’iyyar hamayya ta PDP za ta ba Sanwo-Olu tikitin takarar gwamna idan har APC ta hana shi.

Kara karanta wannan

Jerin ‘yan siyasa 35 da suka fito takara zuwa yanzu, su na hangen kujerar Buhari a Aso Villa

Sai dai kamar da wahala Babajide Sanwo-Olu ya sauya-sheka musamman daga APC zuwa PDP, ko kuma ya raba jiha da mai gidansa a siyasa, Bola Ahmed Tinubu.

GAC ba ta yi zama ba tukuna

Tsoron da ake yi shi ne a samu wani wanda kusoshin APC suke goyon baya a takarar gwamnan. Amma wani ‘dan majalisar GAC ya musanya wannan batu.

A cewarsa, GAC ba ta amincewa Sanwo-Olu neman tazarce ba, kuma ba ta yi wani zama a kan batun ba. Amma dai ana ganin jama’an Legas na tare da shi.

Ko da wanda ya yi takara da Tinubu

Dazu aka ji cewa hadimin gwamnan Legas, Joe Igbokwe ya yi kira na musamman ga wadanda suke shirin yin takara a jam’iyyar APC mai mulki su hakura.

Igbokwe ya ce Bola Tinubu ya kawo mutum siyasa, bai dace ya yi takara da shi ba. Wannan martani ne ga Farfesa Yemi Osinbajo da ke neman tikitin APC.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan APC da ya sha kashi a 2019, ya dawo ya na neman takara a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel