2023: Jerin Mutanen da suka yi farin ciki da ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa

2023: Jerin Mutanen da suka yi farin ciki da ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa

A ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022, mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023. Wannan abu ya yi wa mutane da dama daɗi.

Ayyana shigarsa takara ya kawo ƙarshen watanni da aka kwashe ana yaɗa jita-jitar yana sha'awar gaje kujerar Buhari a 2023, kuma ta ƙara yawan masu hangen muƙamin.

Haka nan kuma lamarin ya sa zai yi gaba da gaba da tsohon Ogansa a jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna alamun manufarsa tun farkon wannan shekara.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da VP Yemi Osinbajo.
2023: Jerin Mutanen da suka yi farin ciki da ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa Hoto: @thacableng
Asali: Twitter

Yayin ayyana takararsa a wani Bidiyo, Osinbajo ya ce:

"A yau, ina mai tawali'u, nake ayyana tsayawa takarar Ofishin shugaban ƙasa a tarayyan Najeriya ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress, APC."

Kara karanta wannan

2023: Bayan samun ƙarin mutum biyu, yan takarar dake hangen kujerar Buhari a PDP sun kai 15

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan lamari dai ya yi wa wasu mutane dadi sosai, mun tattaro muku wasu daga ciki:

1. Magoya baya, Abokai da makusantan Osinbajo

Bayyana wa Duniya shiga tseren takara ya faranta wa magoya baya, abokai da makusantan mataimakin shugabn ƙasa.

Biyo bayan ayyanawarsa, sun yi farin ciki ta hanyar fara bayyana abubuwan alkairan Osinbajo. Ɗaya daga cikin irin waɗan nan abokai shi ne, Richard Akinnola.

Akinnola ɗan asalin jihar Ondo ne kuma abokin Osinbajo wanda ya matsa kan Osinbajo ya fito takara yan makonni kafin ya ayyana a hukumance.

2. Mambobin PDP

Wata tawagar mutane yan Najeriya da ayyana takarar Yemi Osinbajo ta musu ɗaɗi su ne wasu mambobin babbar jam'iyyar hamayya wato PDP.

Wasu ɗaga cikinsu na ganin cewa Mataimakin shugaban hanya ce mai sauki da kowane ɗan takara PDP ta tsayar zai samu nasara cikin sauki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bola Tinubu ya maida martani kan ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa

3. Maƙiyan Tinubu a siyasance

Duk wani hange da zai kawo cikas har Tinubu ya gaza samun Tikitin jam'iyyar APC, labari ne mai matuƙar daɗi ga maƙiyan siyasar tsohon gwamnan Legas ɗin.

Kazalika duk wani ƙalubalen da zai tare wa Tinubu gaba wajen samun tikitin takarar shugaban ƙasa a APC, cigaba ne mai daɗin ji a wurin waɗan nan mutanen.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta ba APC mamaki, ta lashe kujerun Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a Adamawa

Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta cigaba da jan zarenta a zaɓen kananan hukumomi.

Jam'iyya mai mulki ta lallasa abokiyar hamayyarta APC, ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi 21 da kuma Kansiloli 226.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262