Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023
Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, ya bayyana abubuwan da yake so ya yiwa 'yan Najeriya matukar suka bashi dama ya dane kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa
Bayan taron liyafar buda baki da gwamnonin jam'iyyar APC a jiya Lahadi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, TheCable ta ruwaito.
Yayin da yake jawabin ne ya bayyana irin alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya, inda ya ce zai daura daga inda shugaba Buhari zai tsaya a karshen mulkinsa.
Mataimakin shugaban kasar ya ce shirinsa shi ne kafa "Najeriya ta mafarkin mu a cikin 'yan shekaru kadan".
Alkawura 10 da Osinbajo ya yiwa 'yan Najeriya
A jawabinsa, Osinbajo ya bayyana abubuwan da yake son cimmawa idan ya gaji Buhari a zaben 2023 mai zuwa, inda ya ce ya sanya abubuwa kamar haka a gabansa, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro:
- Samar da kyakkyawan yanayi don bunkasa harkar kasuwanci
- Daukaka harkar noma zuwa mataki na gaba musamman wajen amfani da injuna da inganta aikin gona zuwa abu mafi kima
- Tabbatar da cewa gwamnati da hukumominta da masu kula da harkokinta sun yi wa ‘yan kasuwa hidima
- Samar da tattalin arzikin fasaha wanda zai samar da ayyukan yi ga miliyoyi
- Habaka Shirin Zuba Hannun Jari na Jama'a zuwa cikakken tsarin jin dadin rayuwar jama'a
- Kammala alkawarin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin wadannan shekaru goma
- Kammala aikin tabbatar da cewa dukkan 'yan Najeriya maza da mata suna halartar makaranta
- Gyara tsarin karatun mu ya dace da kalubalen wannan karni na 21
- Kammala aikin bayar da tallafin kiwon lafiya ga kowa da kowa
- Da kuma karfafa karfin Jihohi da Kananan Hukumomi wajen gudanar da ayyukansu yadda ya dace
Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023
A wani labarin, daga karshe dai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana nufinsa na neman takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 dake tafe.
Mataimakin shugaban ya ayyana aniyarsa a hukumance ne a wani gajeren Bidiyo da ya saka a shafinsa na Twitter bayan shafe watanni ana rade-radi.
Osinbajo ya ce:
"Ni a yau, tare da matukar kankan da kai ina mai ayyana nufina na neman ofishin shugaban kasan tarayyar Najeriya a hukumance karkashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC)."
Asali: Legit.ng