Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023

  • Bayan dogon lokaci ana raɗe-raɗi, mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shiga takara a hukumance
  • Osinbajo ya ayyana nufinsa a wani sakon bidiyo, ya zayyana nasarorin da ya samu da kuma wanda ya sa a gaba idan ya zama shugaba
  • Mutum na biyu a Najeriya zai fafata da irin su Bola Ahmed Tinubu, mai gidansa a zaben fidda gwani na APC

Abuja - Daga ƙarshe dai mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana nufinsa na neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Mataimakin shugaban ya ayyana aniyarsa a hukumance ne a wani gajeren Bidiyo da ya saka a shafinsa na Twitter bayan shafe watanni ana raɗe-raɗi.

Osinbajo ya ce:

"Ni a yau, tare da matuƙar ƙanƙan da kai ina mai ayyana nufina na neman ofishin shugaban ƙasan tarayya Najeriya a hukumance ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC)."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Amaechi da wasu jiga-jigan APC 4 da Osinbajo zai gwabza da su ya gaji Buhari

"Idan Allah ya yarda kuma mutane suka amince har na samu wannan damar, to ina da yaƙinin cewa abu na farko da zamu mai da hankali shi ne ƙarasa ayyukan da muka ɗakko."
"A hankali zamu gyara tsarin tsaro da kuma kammala garambawul a ɓangaren shari'a. Zamu maida hankali wajen walwalar ma'aikatan shari'a domin tabbatar da an yi wa kowa adalci yadda doka ta tanada."

Cikakken jawabi a Bidiyo

Tarihin siyasar Osinbajo

Osinbajo, wanda ya cika shekara 64 a watan da ya gabata, ya kai matsayin babban lauya (SAN) kuma tsohon malami ne a jami'an Legas. Haka nan shi babban Malami ne a Cocin Redeemed Christian Church of God.

Ya fara riƙe muƙami a gwamnati a shekarar 1998 a matsayin mashawarcin doka ga Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Bola Ajibola, na tsawon shekara hudu.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya, Dr Sani Rijiyar Lemo

A 1999, aka naɗa Farfesa Osinbajo a matsayin Antoni Janar na jihar Legas, lokacin gwamna, Bola Ahmed Tinubu, kuma ya cigaba da zama a kujerar har zuwa 2007.

Haka nan an zaɓi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari a 2014 kuma suka samu nasara a zaɓen 2015.

Mataimakin shugaban ƙasan ya rike muƙaddashin shugaban ƙasa a lokuta daban-daban na tsawon kwana 120 yayin da Buhari ya tafi Landan duba lafiya tsakanin 2016 da 2018.

A wani labarin na daban kuma bayan Tambuwal, Bala Muhammed da Wike, wani gwamnan PDP ayyana aniyar shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel , ya amsa kiran yan Najeriya na neman takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamnan ya ce ya karbi Fam ɗin da wata kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta siya masa na sha'awar takara a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262