Ramadaniyyat 1443: Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya, Dr Sani Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya, Dr Sani Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Wannan karo, Malam ya yi magana da abubuwan da ke hana Musulmi yin karya

Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya

Ҝarya wata mummunar halayya ce. Duk wanda aka san shi da ƙarya yakan rasa samun yardar mutane har abada. Don haka, a kowace shari'a aka haramta yin ƙarya. Kuma duk ilahirin masu hankali sun haɗu a kan ganin muninta.

Akwai abubuwa da dama da suke hana mutum ya riƙa yin ƙarya da gangan, ga wasu kaɗan daga ciki:

Na ɗaya, Imani da Allah da ayoyinsa da tsoron haɗuwa da shi ranar alƙiyama, Allah (SWT) yana cewa: (Waxanda ba sa yin imani da ayoyin Allah su ne kawai suke ƙirƙirar ƙarya..). [Suratut Nahl, 105]. Saboda haka riƙo da addini babbar garkuwa ce daga yin ƙarya.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Ko da Mun Yi Saɓani, Daga Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Na biyu, guje wa zubewar mutunci, kamar abin da ya faru lokacin da Hiraƙal shugaban Rumawa ya sa aka kirawo masa Abu Sufyan sarkin Makka da muƙarrabansa, a lokacin bai musulunta ba, ya yi masa tambayoyi game da Annabi (SAW) ya kuma sanar da mabiyan Abu Sufyan cewa, da zarar ya yi ƙarya, su fallasa shi. Don haka, duk abin da Hiraƙal ya tambaye shi game da Annabi SAW sai da ya faɗa masa gaskiya, bai voye masa komai ba, ko ya canza masa, har ma yana cewa: "Na rantse da Allah, ba don gudun kunyar su kama ni na tava yin ƙarya ba, da na yi masa ƙarya". [Bukhari#7].

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr Sani Rijiyar Lemo
Ramadaniyyat 1443: Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya, Dr Sani Rijiyar Lemo
Asali: Facebook

Na uku, gudun cutuwa ta fuskar duniya. Wannan shi ne babban dalili da za ka iya samu tare da masu manyan sana'o'i, watau sukan guji yi wa abokan hulɗarsu ƙarya don gudun kada su fahimci suna yi musu ƙarya su canja abokan harƙalla. Don haka, sukan tsaya a kan faɗar gaskiya don guje wa wannan illa. Hakanan ma masu ƙananan kasuwanci, sau tari su ma suna yin gaskiya don sana'arsu ta ɗore kada ƙarya ta ta jawo musu koma-baya a sana'arsu.

Kara karanta wannan

Kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU ta gindaya sharuddan da zasu sa ta janye yajin aiki

Na huɗu, mutumin da ya tashi tun yarinta da neman ilimi, yake kuma fatan kai wa wani matsayi da mutane zu su yarda da shi, su amince da duk wata magana za ta fito daga bakinsa. To irin wannan yakan yi kaffa-kaffa wajen jefa kansa cikin yaɗa labaran ƙarya, don gudun kada iliminsa ya tafi a banza, mutane su daina yarda da shi. Babban Malamin hadisin nan Abdurrazzaƙ As-Sana'ani yana cewa, "Na je aikin hajji, na yi kwana uku babu wani ɗalibin hadisi da ya zo neman hadisi wajena, sai na tafi Ka'aba na yi ɗawafi, na kama rigar Ka'aba ina cewa, Ya Ubangiji, mene ya same ni, shin ni maƙaryaci ne, ko kuma ni mai Tadlisi ne? Sai na dawo gida, sai kuma ga shi sun zo mani". [Ibn Asakir, juzu'i na 36, shafi na 179].

Don haka malaman hadisi suke guje wa ƙarya don kada su bata ilimin da suka yi shekara da shekaru suna tarawa.

Allah ya sa mu dace. Amin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel