Wa ya sani ko yan Najeriya ni suke kaunar na gaji Buhari a 2023? Fayose ya ce ba zai janye daga takara ba

Wa ya sani ko yan Najeriya ni suke kaunar na gaji Buhari a 2023? Fayose ya ce ba zai janye daga takara ba

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, yace ba bu wani zancen sulhu da zai sa ya janye wa wani takararsa ta zama shugaban kasa
  • Fayose, ya ce ba bu wanda yasan abin da ke zuciyar yan Najeriya, wataƙila shi suke kaunar ya zama shugaba a 2023
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya ce wajibi jam'iyya ta kai takara yankin kudancin Najeriya

Ekiti - Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce ba zai janye wa wani ɗan siyasa a PDP takarar da yake na zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023.

Fayose ya yi wannan furucin ne a wata zanta wa da kafar watsa labarai ta Channels TV ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu, 2022.

Da yake jawabi a cikin shirin, tsohon gwamnan ya ce tuni ya lale kuɗi ya sayi Fam ɗin sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa wajibi PDP ta kai tikiti yankin Kudu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu

Tsohon gwamnan Ekiti, Fayose.
Wa ya sani ko yan Najeriya ni suke kaunar na gaji Buhari a 2023? Fayose ya ce ba zai janye daga takara ba Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Fayose ya ce:

"Ba na layin masu ganin a watsar da tsarin karɓa-karɓa a batun kujerar shugaban ƙasa. Ina cikin mambobin kwamitin karba-karba har zuwa ranar ƙarshe da na sayi Fam."
"Abin da suka ce tunda jam'iyya ta riga ta fara da daɗewa kuma mutane sun siya Fam, saboda haka mai yuwuwa PDP ta zauna dan yin sulhu, ba wanda yace a bar ƙofa a buɗe."
"Hanya ɗaya da za'a warware wannan matsalar ta yanki shi ne kada wani ɗan arewa ya shiga zaɓen fidda gwani, wanda muka yi a Patakwal duk yan arewa ne, me zai sa yan kudu ba zasu yi na su ba?"

Mista Fayose ya ce abu ɗaya da zai sa ya amince da zaɓin yin sulhu shi ne idan shi jam'iyyar PDP zata tsayar takara, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin sharuddan da INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa, ta shirya fatali da yan takara a zaɓen 2023

Shin tsohon gwamnan zai iya kawo wa PDP nasara?

Da aka tambaye shi, wane shiri gare shi da zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa karkashin PDP a 2023, Fayose yace:

"Yan Najeriya ne kaɗai zasu yanke wanda zai samu nasara a zaɓe. Ta ya na lallasa gwamnoni ma su ci na kwashe zango biyu a mulkin Ekiti? Rayuwa tana farawa daga wani wuri."
"Wa ya sani idan yan Najeriya ni suke son zaɓa? Kunsan abinda ke zuƙatan su ne? Kunsan me suke so? Duk wani taro da suka yi maganar sulhu, ba zancen demokaradiyya a ciki."

A wani labarin kuma Daga karshe, Gwamna Ortom ya fayyace yankin da PDP zata ba takarar shugaban ƙasa a 2023

Shugaban kwamitin karba-karba na jam'iyyar PDP ya musanta rahoton cewa sun buɗe kofa kowa ya nemi takara a zaɓen 2023.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce sun kammala aikinsu kuma sun kai wa NEC rahoto, wuƙa da nama na hannunta.

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262