Sabon Rikici: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya yi barazanar maka PDP a Kotu kan kuɗin Fam
- Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin PDP, Ayoola Falola, ya koka kan yadda jam'iyya ta cika kuɗin Fam ɗinta
- Mista Falola ya yi zargin cewa miliyan N40m da PDP ta sanya ya yi yawa duba da halin ƙaƙanikayi da ake ciki a ƙasa
- A cewarsa, yana zargin PDP ta saka waɗan nan makudan kuɗin ne domin ba masu kuɗi kaɗai dama kuma hakan ya saɓa wa doka
Abuja - Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Ayoola Falola, ya bayyana makudan kuɗin da jam'iyya ta sa na kuɗin nuna sha'awa da son zuciya don masu kuɗi.
Leadership ta rahoto cewa ɗan takarar ya yi barazanar ɗaukar matakin doka kan jam'iyya, "idan ba'a yi gaggawar shawo kan lamarin ba kuma aka ƙi yin adalci."
Falola, wanda ya yi bayanin shi mamba ne na PDP a gunduma ta 12, karamar hukumar Ibadan South West a jihar Oyo, ya tura korafi kai tsaye ga shugabancin jam'iyya na ƙasa.
A cewarsa, makudam kuɗin da aka sa wa Fam ɗin bai yi kama da matsanancin rashin kuɗin da ake fama da shi a Najeriya ba a yanzu.
Ya kuma ce yana ganin an tsananta kuɗin Fam din ne domin, "Rage yawan yan takara ko bin wata hanyar rashin adalci wajen fifita wasu tsiraru."
Shin nawa PDP ke cefanar da Fam ɗin?
Idan baku mance ba, babbar jam'iyyar hamayya ta sanya kuɗin Fam na nuna sha'awar tsayawa takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya miliyan N40m.
Zuwa yanzun, yan takara 14 da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni masu ci, da yan kasuwa sun lale waɗan nan kuɗaɗe sun karbi Fam.
Sai dai a ganin Falola:
"Wannan kuɗin da aka sanya wa Fam ɗin nuna sha'awa wata hanya ce kawai ta tabbatar da masu kuɗi ne kaɗai zasu siya, kuma hakan ya saɓa wa kudiri da manufar da aka kafa jam'iyya."
A wani labarin kuma Babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauya sheka zuwa APC mai mulki
Tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Gombe, Barista Abdulƙadir Yahaya, ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC mai mulki.
Tsohon mashawarci kan harkokin siyasa ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda ɗumbin ayyukan cigaba da gwamna ke yi.
Asali: Legit.ng