Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni

Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni

  • Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwaryan APC ya bayyana nasarar da jam'iyyar ta samu karkashinsa
  • Buni wanda ke shirin mike mulki ga duk wanda aka zabe yau, yace sun yi ayyuka tukuru don hadin kan jam'iyyar
  • Kawo yanzu, an saki jerin sunayen wadanda aka yi ittifaki kansu su zama sabbin shugabannin jam'iyyar

Abuja - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa adadin mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya tashi daga 11million zuwa 41 million.

Buni, wanda shine shugaban jam'iyyar mai barin gado ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wajen taron gangamin jam'iyyar a Abuja, rahoton Vanguard.

Ya ce da yiwuwan adadin mambobin ya sake tashi daga milyan 41 saboda har yanzu ana rijista.

Buni ya ce kwamitin rikon kwaryarsa ta samu nasarar sulhunta dimbin 'ya'yan jam'iyyar kuma ya janyo gwamnoni uku jam'iyyar daga PDP.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Sarkin Musulmi ya yi gargadi kan kara farashin kayan masarufi

Gwamnonin a cewarsa sun hada da na Zamfara, Cross Rivers da Ebonyi.

Mai Mala Buni
Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni Hoto: @APCNationalConvention2022
Asali: Twitter

An radawa sakariyar APC sunan Buhari

Buni yace sun kammala aikin gyara hedkwatar jam'yyar kuma sun biya bashin kudin hayan da ake binsu.

Bayan haka, Buni yace sun sanyawa ginin sunan Shugaba Muhammadu Buhari bisa jagorancin kwarai da yayi.

Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabbatar da cewa jam'iyyar All Progressives Congress ta zabi tsohon gwamna, Abdullahi Adamu, matsayin wanda za'a zaba sabon shugabanta.

Sule ya bayyana hakan da yammacin Juma'a yayin hira a shirin Politics Today na tashar ChannelsTV.

Gwamnan wanda yayi magana kan shirye-shiryen da jam'iyyar ke yiwa taron gangamin gobe Asabar, ya ce dokar zabe ta amince da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng