2023: Shugabannin PDP Na Kudu Sun Yi Taro, Sun Ce Dole Shugaban Kasa Ya Fito Daga Yankinsu
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen Kudu maso yamma ta ce yankin Kudu ne ya kamata ta fitar da shugaban kasa a 2023
- Jiga-jigan jam'iyyar na PDP sun bayyana hakan ne bayan taron da suka yi a gidan gwamnati, Agodi, Ibadan, Jihar Oyo
- Jam'iyyar ta PDP ta ce idan dai ana son adalci ya kamata a bawa yankin na kudu damar fitar da shugaban kasa kamar yadda kungiyar gwamnonin kudu ta nema
Ibadan - Jiga-jigan jam'iyyar PDP na Kudu maso Yamma su yi taro a ranar Talata, inda suka yanke shawarar cewa daga yankin kudu ya kamata jam'iyyar ta fitar dan takarar shugaban kasa.
Wanann na daga cikin batutuwan da aka amince a kansu a karshen taron na jiga-jigan jam'iyyar PDP reshen Kudu maso Yamma da aka yi a gidan gwamnati, Agodi, Ibadan, rahoton Daily Trust.
Shugaban jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, Cif Soji Adagunodo, ya karanta sakon bayan taro.
Muna goyon bayan gwamnonin kudu, jiga-jigan PDP na kudu maso yamma
Ya yi bayanin cewa jam'iyyar ta PDP reshen kudu maso yamma tana goyon bayan kungiyar gwamnonin kudu na neman ganin shugaban kasa na gaba ya fito daga kudu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Adagunodo ya cigaba da cewa jam'iyyar ta yanke shawarar cewa dukkan mambobinta su yi aiki don ganin sun yi nasara a zaben Osun da Ekiti.
"Mun yanke shawarar cewa hadin kan kudu maso yamma ya fi komai muhimmanci; don haka muna kira ga cewa a mayar da hankali wurin warware matsaloli.
"Yankin tana neman ganin an yi adalci wurin rabon mukamai na tarayya da nade-nade.
"Za mu goyi bayan dukkan kokarin da ake yi na hadin kai wurin rabon mukamai da nade-nade a yankuna," a cewar sanarwar bayan sakon.
Wadanda suka hallarci taron
Tsaffin gwamnoni daga yankin, Ayodele Fayose, (Ekiti); Olagunsoye Oyinlola (Osun); Olusegun Mimiko (Ondo); sun hallarci taron.
Sauran manyan bakin da suka hallarci taron sun hada da Seyi Makinde; mataimakin jam'iyyar na kasa, Taofeek Arapaja, Bode George, tsohon mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Olusola Eleka da Sanata Francis Fadahunsi daga Osun.
Sabon Ƙalubale Na Jiran Kwankwaso Idan Ya Bar PDP Zuwa NNPP, Zai Ci Karo Da Abokan Takara 15
A wani labarin, sakataren watsa labaran jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Ambasada Agbo Majo ya ce yanzu haka akwai ‘yan takarar shugaban kasa 15, masu takarar sanata, ‘yan majalisar tarayya da na jiha da dama da suke son tsayawa karkashin jam’iyyar.
Ambasa Agbo ya ce jam’iyyar tana shirin yin gamgamin ta na gaba daya kasar nan a ranar 30 ga watan Maris wanda za su yi a Abuja, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Yayin yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata a garin Abuja, sakataren watsa labaran ya ce NNPP tana shirin kawo gyaran da ba a tana kawowa ba a kasar nan.
Asali: Legit.ng