Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da bukatar gwamna Umahi da aka kwace kujerarsa
- Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta yi fatali da bukatar gwamna Umahi, mataimakinsa da yan majalisa 16
- Alkalin Kotun ya sanar da cewa ya ɗauki matakin ne biyo bayan janye wa da masu shigar da bukatar suka yi
- Kotu ta tsige gwamna, mataimakinsa, da yan majalisa 16 bisa sauya sheka daga PDP zuwa APC, kuma suka bukaci ta dakatar da hukuncin
Abuja - Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da bukatar gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, mataimakinsa da yan majalisu 16 na tsayar da batun sauke su daga kan mulki.
Daily Trust ta rahoto cewa Alkalin Kotun, Mai Shari'a, Inyang Ekwo, shi ne ya yanke hukunci bayan masu ƙara sun janye bukatarsu.
The Nation ta rahoto Alƙalin ya ce:
"Bayan samun bayanan ɗaukaka ƙara, da kuma bukatar janye batun dakatar da zartar da hukunci daga masu ƙara, Kotu ta yi watsi da lamarin."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar 8 ga watan Maris, Kotun ta kwace kujerar gwamna, mataimakinsa da yan majalisun kan sauya shekar da suka yi daga jam'iyyar PDP zuwa All Progressive Congress (APC).
Dukka kusoshin gwamnatin da lamarin ya shafa sun shigar da bukatar dakatar da zartar da hukuncin kwace kujerunsu a babbar Kotun da kuma takardar ɗaukaka ƙara a Kotun ɗaukaka ƙara dake zaune a Abuja.
Yadda zaman Kotu ya gudana
Tun da farko Lauyan gwamna Umahi, Chukwuma Machukwu Ume (SAN), shi ne ya gabatarwa Kotu matakinsu na janye bukatar da suka shigar.
A cewarsa, a halin yanzu babu bukatar tafka muhawara kan bukatar a nan domin sun shigar da lamarin a bayanan da suka miƙa wa Kotun ɗaukaka kara.
A nasa ɓangaren Lauyan jam'iyyar PDP, Emmanuel Ukala (SAN), bai yi gardama kan lamarin ba, amma ya roki Kotun ta soke bukatar baki ɗaya.
A wani labarin na daban kuma Mafarauci ya bindige tsohon shugaban APC har Lahira, ya ce ya ɗauka wata dabba ce
Wani maharbi ya bindige tsohon shugaban jam'iyyar APC na wata gunduma a jihar Enugu bisa kuskure ranar Asabar.
Jama'an gari sun ɗora wa Fulani makiyaya laifin, amma daga baya aka gano cewa wani Mafarauci ne ya aikata kisan.
Asali: Legit.ng