Shirin 2023: PDP ta sa ranar zaben fidda gwani na 'yan takarar shugaban kasa, da farashin fam
- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta saki jadawali da ayyukanta na babban zaben 2023
- PDP ta amince da fara siyar da fam din zaben fidda gwanin jam’iyyar daga ranar Alhamis, 17 ga watan Maris
- Za ta siyar da fam din takarar shugaban kasa da na nuna ra’ayin takara kan naira miliyan 35 da naira miliyan 5
Abuja - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye domin gudanar da taron fidda dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 a watan Mayu.
A cewar wasu majiyoyi abin dogaro, ana iya gudanar da taron a ranar 28 da 29 ga watan Mayun 2022, jaridar Vanguard ta rahoto.
Da yake jawabi ga manema labarai a karshen taron majalisar zartarwa ta jam’iyyar a ranar Talata, sakataren labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce PDP ta kammala shiri tsaf domin babban zaben 2023.
A cewar Umar Bature, sakataren shirye-shirye na kasa, za a fara siyar da dam din takara daga ranar Alhamis, 17 ga watan Maris.
A wata sanarwa da aka fitar a karshen taron, jam’iyyar ta amince da siyar da fam din takarar shugaban kasa da na nuna ra’ayin takara kan naira miliyan 35 da naira miliyan 5.
Hakazalika, fam din takarar gwamna zai tafi kan naira miliyan 20 yayin da fam din nuna ra’ayin takara zai tafi a naira miliyan 1.
Sauran da suka hada da majalisar dokokin jiha – fam din nuna ra’ayi N100,000 sannan fam din takara kan N500,000.
Vanguard ta kuma rahoto cewa fam din takarar dan majalisar wakilai naira miliyan 2 sannan na nuna sha’awar takar N500,000, na majalisar dattawa naira miliyan 3 sannan na nuna sha’awa N500,000.
Babu shiri, dole Shugaban PDP ya tada taro saboda za a kawo tashin hankali kan tutar 2023
A wani labarin, mun ji a baya cewa rudani ya shiga cikin babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a daren ranar Litinin, wanda hakan ya jawo Dr. Iyorchia Ayu ya dage zaman da ake yi.
Jaridar The Nation ta ce an samu sabani a jam'iyyar PDP yayin da wasu ‘yan siyasar Kudu suka nemi a hana duk wanda ya sauya-sheka tikitin yin takara.
‘Yan siyasar sun hakikance a kan cewa duk wanda ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC a baya, bai cancanci ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.
Asali: Legit.ng