Shugabancin APC: Tsohon gwamnan Zamfara ya yi fatali da tsarin yanki, ya lale miliyan N20m na Fom
- Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul-Aziz Yari ya saya Fom ɗin takarar shugaban APC duk da kai kujerar Arewa ta tsakiya
- Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin rarraba muƙaman shugabannin jam'iyya, yayin da babban taronta na ƙasa ke matsowa
- A ranar 26 ga watan Maris, 2022, APC ke sa ran gudanar da babban taron kamar yadda ta tsara
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, a ranar Laraba a Abuja, ya sayi Fom ɗin takarar shugaban jam'iyyar APC yayin da babban taro na ƙasa ke karatowa.
Punch ta ruwaito cewa jam'iyyar APC ta sanya ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban taronta na ƙasa wanda za'a zaɓi shugabannin jam'iyya.
Wannan na zuwa ne duk da tsarin rarraba muƙamai da APC ta fitar, wanda ya tura kujerar shugaba zuwa yankin arewa ta tsakiya.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane sanye da riga mai ɗauke da hoton Yari ne suka mamaye Sakatariyar APC ta ƙasa domin karbar wa tsohon gwamnan Fam na takara.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala siyan Fam ɗin a madadin ƙungiyar magoya bayan Yari, Sanata Tijani Kaura, ya ce Abdul-aziz Yari cikakken ɗan jam'iyya ne kuma kujerar shugaba ta yan arewa ce.
Premium times ta rahoto A jawabinsa ya ce:
"Yanzun muka karɓar wa Sanata Abdul-Aziz Yari Fam domin ya nemi kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa."
Meyasa ya siya Fam bayan kujerar ta Arewa ta tsakiya ce?
Da aka tambaye shi, ko Yari ya yi fatali da tsarin rarraba muƙamai zuwa yanki-yanki shiyasa ya saya Fam, Sanata Kaura ya ce:
"A iya abun da muka sani, an samu sabani kan tsarin raba mukamai zuwa yanki. Da farko mun san cewa an miƙa kujerar shugaban jam'iyya arewa, ɗan takarar shugaban ƙasa kudu."
"Abin da kowa ya sani shi ne duk wata kujera dake Kudu a baya za'a maida ta hannun yan arewa, haka na arewa za'a maida su kudu, dan haka Zamfara na Arewa."
A wani labarin kuma Tsagin Mala Buni ya kwace ikonsa a Hedkwatar APC, ya faɗi gaskiyar abun da ya faru
Kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Gwamna Buni na Yobe ya sake dawo da ƙarfinsa a hedkwatar APC ta ƙasa.
Sakataren kwamitin na kasa, Sanata Akpanudoedehe, ya koma bakin aiki bayan jita-jitar ya yi murabus ko an canza shi.
Asali: Legit.ng