2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki

2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya umarci duk wadanda ya nada a mukamai daban-daban da sauran ma’aikatan gwamnati masu takara da su yi murabus
  • A cewarsa, wajibi ne su sauka daga mukaman su a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022 ko kafin nan, yayin da zaben 2023 yake kara matsowa
  • Ya sanar da hakan ne ta wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas ya saki kuma ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba

Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci duk wadanda ya nada mukamai na gwamnati da sauran ma’aikata da su yi murabus zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2022 ko kuma kafin nan yayin da zabe yake karatowa.

Ya shaida hakan ne ta wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas ya saki wacce wakilin The Punch ya gani a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shawaran Masari ga masu rike da mukamai: Ku ajiye mukamanku kafin takara

2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Rike Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki
2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Rike Da Mukaman Gwamnati Da Ke Son Takara Su Ajiye Aikinsu. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Takardar ta tunatar da wadanda lamarin ya shafa cewa sabuwar dokar zabe ta bukaci duk wasu ma’aikatan gwamnati da su yi murabus daga mukaman su don tsayawa takarar zabe mai zuwa.

Kamar yadda takardar ta nuna, babban hadimi na musamman, manyan masu bayar da shawarwari da kuma sauran masu manyan mukamai na gwamnati su bi dokar bisa wannan umarnin.

Sabuwar dokar zabe ta hana mai mukamin gwamnati tsayawa takara

Ta kula da cewa dokar ta nemi duk masu burin takara da su yi murabus ana saura kwana 30 zaben fidda gwani na jam’iyyar da mutum zai tsaya takara.

Kamar yadda takardar ta shaida:

“Zuwa yanzu, bisa umarnin wannan dokar, wajibi ne duk wadanda aka nada mukamai da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da suke da kudirin takara da su rubuta takardar murabus ga sakatarn gwamnatin jihar, SSG a ranar 31 ga watan Maris na 2022 ko kafin sannan.”

Kara karanta wannan

Kotu Ta Goyi Bayan Dokar Hana Saka Hijabi a Indiya, Ta Ce Babu Addinin Da Ya Wajabta Saka Hijabin

Idan ba a manta ba, sashi na 84 (12) na dokar zabe wanda shugaban kasa Manjo Janar Muhammadu Buhari mai murabus ya sanya hannu, ta hana duk wani mai mukami da ke kasar nan takara tun daga zaben fidda gwani, ba tare da ya yi murabus ba.

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

A wani labarin, Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar Kaduna, Muhammad Dattijo, ya bayyana kudirin sa na maye gurbin Gwamna Nasir El-Rufai a 2023, The Punch ta ruwaito.

Dattijo, wanda makarantar kasuwanci ta Henley da ke Jami’ar Reading a Ingila ba ta dade da ba shi mukami ba a cibiyar Dunning Africa, ya shaida hakan a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Talata.

Kamar yadda ya bayyana:

“Na yi wannan wallafar ne don sanar da niyyata ta fara kamfen din neman kujerar gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 da ke karatowa.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164