Shugabancin APC: Ban Taɓa Shan Kaye a Zaɓe Ba Tunda Na Shiga Siyasa Kimanin Shekaru 50 Da Suka Shuɗe, Adamu

Shugabancin APC: Ban Taɓa Shan Kaye a Zaɓe Ba Tunda Na Shiga Siyasa Kimanin Shekaru 50 Da Suka Shuɗe, Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa ya bayyana cewa bai taba fadi zabe ba tunda ya shiga siyasa a 1970s
  • Sanata Adamu ya yi wannan furucin ne yayin ganawa da mambobin jam'iyyar APC na majalisar wakilai na tarayya game da takararsa na shugabancin APC
  • Sanata Adamu ya sanar da yan majalisar cewa ya yi jinkirin bayyana ra'ayinsa na yin takarar ne domin yana can yana aikin sulhunta yan APC a jihohi daban-daban

FCT, Abuja - Sanata Abdullahi Adamu, daya daga cikin masu takarar shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa ya ce tunda ya shiga siyasa a 70s bai taɓa fadi zabe ba.

Daily Trust ta rahoto cewa tsohon gwamnan na Nasarawa, kuma sanata mai ci a yanzu, ya samu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari bisa takarar da ya ke yi.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Shugabancin APC: Ban Taɓa Shan Kaye a Zaɓe Ba Tunda Na Shiga Siyasa a Kimanin Shekaru 50 da Suka Shuɗe, Adamu
Shugabancin APC: Ban Taɓa Fadi Zaɓe Ba Tunda Na Shiga Siyasa a Kimanin Shekaru 50 da Suka Shuɗe, Adamu. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aikin sulhunta 'yan APC yasa na jinkirta bayyana niyya ta na yin takarar shugaban APC, Adamu

Da ya ke magana yayin da ya ke gana wa da yan majalisun wakilan tarayya na APC, a ranar Talata, ya ce bai sanar da takararsa da wuri ba saboda yana ta aikin sulhunta yan jam'iyyar a kasa.

A cewarsa, yana ta aiki tare da kwamitin sulhun na jam'iyyar da aka daura wa nauyin sulhunta wadanda suke da matsaloli hakan yasa bai sanar da aniyarsa da wuri ba, rahoton Daily Trust.

A 2021, APC ta naɗa Adamu a matsayin shugaban kwamitin sulhu na mutum 9. Ya zaga sassan kasar da dama domin ganawa da yan jam'iyyar wadanda suke da korafi.

Ya shaidawa yan majalisar cewa duk da cewa shine na karshen sanar da takararsa, a shirye ya ke ya fuskanci matsalolin da jam'iyyar ke fama da su.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

Ya kara da cewa bai taba yin takara ya faɗi ba tunda ya shiga siyasa a 1970s.

Abin da shugabannin APC a majalisa suka cewa Sanata Adamu

Tunda farko, jagoran a majalisa, Alhassan Ado Doguwa, wanda ya tarbi Sanata Abdullahi Adamu, ya yaba masa, yana cewa shi kwararren dan siyasa ne kuma ya cancanci jagorancin jam'iyyar.

Ya ce duk da cewa sauran yan takarar sun sanar da yan majalisar cewa za su ziyarce su, Sanatan ne na farko da ya kawo musu ziyara.

A bangarensa, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase ya ce Sanata Adamu mutum ne mai kaifin hankali wanda ke da niyyar kawo kwarewarsa ta siyasa a lokacin da ake bukatarta.

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

A wani labarin, Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar Kaduna, Muhammad Dattijo, ya bayyana kudirin sa na maye gurbin Gwamna Nasir El-Rufai a 2023, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Labari da Ɗuminsa: Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF, Ta Yi Babban Rashi

Dattijo, wanda makarantar kasuwanci ta Henley da ke Jami’ar Reading a Ingila ba ta dade da ba shi mukami ba a cibiyar Dunning Africa, ya shaida hakan a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Talata.

Kamar yadda ya bayyana:

“Na yi wannan wallafar ne don sanar da niyyata ta fara kamfen din neman kujerar gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 da ke karatowa.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164