Siyasar Kaduna: ‘Yan gaban-goshin gwamna El-Rufai da za su kawo wanda zai gaji mulki

Siyasar Kaduna: ‘Yan gaban-goshin gwamna El-Rufai da za su kawo wanda zai gaji mulki

  • Har an fara tseren wanda zai gaji kujerar Nasir El-Rufai a karkashin jam’iyyar APC a jihar Kaduna
  • Akwai wasu mutane 11 zuwa 14 da ake tunanin daga cikinsu ne za a samu sabon gwamna a Mayun 2023
  • A wannan jerin akwai ‘yan gaban goshi akwai ‘yan majalisar tarayya, kwamishinoni da hadiman gwamna

Kaduna - Akwai wasu ‘yan cikin gida a gwamnatin Nasir El-Rufai da ake tunanin su ne za su fito da wanda zai zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023.

Wata majiya daga gidan Sir Kashim Ibrahim ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa akwai wasu mutane 11 da ke kusa da madafan ikon gwamnatin Kaduna.

Da aka yi hira da Mallam El-Rufai a gidan talabijin Channels TV a makon da ya gabata, gwamnan ya bayyana cewa yana tare da majalisar da ke zagaye da shi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Gwamna El-Rufai ya tabbatar da cewa akwai wasu mutanen da suke tare da shi tun 2014. Da wadannan kusoshi ne APC ta iya lashe zabukan 2015 da 2019.

Jaridar ta bibiyi wadannan ‘yan gaban goshin Gwamna tun daga mataimakiyarsa zuwa wasu hadimai.

1. Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe

Mai girma mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ita ce ta farko a majalisar El-Rufai. Balarabe ta fito ne daga yankin Kudancin jihar.

2. Balarabe Abbas Lawal

Na biyu a jeringiyar shi ne Balarabe Abbas Lawal wanda yanzu yake rike da kujerar sakataren gwamnati. Kusan da shi ake yin duk wasu kulle-kulle a gwamnatin.

3. Muhammed Sani Abdullahi

Daily Trust ta ce akwai kwamishononi uku a wannan jeri. Na farko a cikinsu shi ne tsohon shugaban ma’aikatar gidan gwamnati wanda aka fi sani da Dattijo.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

Gwamna El-Rufai
Malam Nasir El-rufai a ofis Hoto: Governor Kaduna
Asali: Twitter

4. Bashir Saidu

Bayan Muhammed Sani Abdullahi kuma akwai wani kwamishina mai karfi a Kaduna watau Bashir Saidu. Da alamun cewa yana cikin wadanda za su nemi gwamna.

5. Samuel Aruwan

Wani Kwamishina da yake cikin ‘yan-lelen gwama Nasir El-Rufai shi ne na harkokin tsaron cikin gida. Samuel Aruwan ya rike kakakin gwamna daga 2015 zuwa 2019.

6. Sanata Uba Sani

A wannan majalisa akwai wasu Sanatoci masu-ci a Kaduna. Na farko a jerin Sanatocin shi ne Uba Sani. Kafin zaben 2019, shi ne mai bada shawara a harkokin siyasa.

7. Sanata Suleiman Abdu Kwari

Suleiman Abdu Kwari mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar datttawa yana cikin wadanda ake rufe kofa da su a gwamnati, da su ne ake duk kulle-kulle a APC.

8. Jimi Lawal

Jimi Lawal wanda babban mashawarci ne a gwamnati, yana da kunnen Mai girma Nasir El-Rufai.

9. Hafiz Bayero

A cikin matasan da ake damawa da su a jihar Kaduna akwai Hafiz Bayero mai rike da cikin birni.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

10. Muyiwa Adekeye

Mai magana da yawun bakin gwamna, Muyiwa Adekeye yana cikin matasan da ake tafiya da su.

11. Saude Atoyebi

A karshe akwai mataimakiyar shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Saude Atoyebi a wannan rukuni.

Rahoton ya ce Idris Othman, Hadiza Bala Usman da Peter Jones su na cikin wadanda ake jin maganarsu. Watakila su na da ta-cewa a game da siyasar Kaduna.

Zaben Kaduna

Kwanaki mun kawo maku rahoto cewa ana tunanin tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Sani Abdullahi zai nemi gwamna. A yau hakan ta tabatta.

Bayan wadannan fitattun 'yan siyasa, shugaban hukumar nan ta NIMASA, Bashir Yusuf Jamoh ya na cikin wadanda ake yi wa ganin harin gwamna a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng