2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa zai sanar da aniyarsa ta yin takarar kujerar Buhari a hukumance nan ba da jimawa ba
  • Saraki ya bayyana cewa a halin yanzu, suna kan tuntuba tare da tawagarsa a fadin kasar
  • Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya kuma ce yana jira ya ga yankin da PDP za ta mikawa tikitinta na takarar shugaban kasa ne kafin ya yunkura

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ce zai ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a zaben 2023 a hukumance bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tsayar da yankin da za ta baiwa tikitinta.

Saraki wanda ya zanta da manema labarai a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris, ya ce zai ayyana aniyarsa ta yin takara a karshen watan Maris, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tsayar Da Jonathan Takara Zai Kwantar Da Tarzomar Kudu Maso Gabas, Ƙungiya

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukol saraki
Bukola saraki ya ce zai sanar aniyarsa nan ba da dadewa ba Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

A yayin shirin, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya yi ikirarin cewa yana da abun da ake bukata domin jagorantar Najeriya.

Saraki ya kuma ce shi da tawagarsa sun karade kasar domin tuntubar masu ruwa da tsaki a kan kudirinsa na takarar shugaban kasa, rahoton Punch.

Ya ce:

“Kamar kowa, akwai ka’idoji, akwai matakai.
“Za mu yi taron NEC na PDP a ranar Talata. Muna sanya ran tsare-tsaren za su bayyana wanda zai nuna mana daga ina za mu fara.
“Shakka babu zan sanar da wani abu kafin karshen wata, aniyata ta neman takarar shugaban kasa. A halin yanzu, tuntuba kawai muke yi. Za mu ayyana a hukumance idan lokaci ya yi.
“Na yi imani ina da abubuwan da ake bukata domin jagorantar Najeriya. Ni ba mutum ne mai gudun gwada sa’arsa ba. Ni ba mutum ne da bai san lamura ba ko mutumin da bai da kuzarin magance wadannan lamura ba.

Kara karanta wannan

Farin Jakada: Jarumin Kannywood Ahmad Lawan ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

“Bugu da kari, ni mutum ne da zai iya aiki da kowa a fadin jam’iyyun siyasa, duba ga abubuwan da na riga nayi. Ni mutum ne da zai iya isa ga dukka kabilu da addinai.”

Saraki ya bukaci yan Najeriya da su damu da zabar mutumin da zai iya magance matsalolin kasar maimakon tsarin karba-karba.

Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara

A wani labarin, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na shirin kalubalantar sauya shekar gwamnonin Sokoto, Benue da na Edo zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wannan yunkurin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na tsige Gwamna Dave Umahi daga kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa APC bayan an zabe shi a karkashin inuwar PDP.

APC na ganin za ta fi cin riba idan har aka aiwatar da irin haka a kan gwamnonin da wasu shugabannin PDP da aka zaba a karkashin inuwarta.

Kara karanta wannan

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng