Babbar magana: Kotu ta hana APC gudanar da taron gangaminta na kasa na 26 ga Maris
- Wata kotu a Abuja ta dakatar da jam'iyyar APC daga gudanar da taronta na gangami sai har an yi zaman shari'a
- Wannan na zuwa ne yayin da kwanaki kadan suka rage jam'iyyar ta gudanar da taron gangaminta na kasa
- A baya INEC ta tura wasika ga jam'iyyar APC domin sanar da ita kuskuren da ta yi wajen taka dokar hukumar ta INEC
Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta hana jam’iyyar APC ci gaba da gudanar da taronta na gangami na kasa har sai an saurari karar da aka shigar kan jam’iyyar da ke gaban kotun, inji rahoton Daily Sun.
Salisu Umoru ne ya shigar da karar mai lamba FHC/HC/CV/2958/2021, inda ya ja jam’iyyar da shuganta na riko, Mai Mala Buni da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin kalubalantar taron gangamin da aka shirya.
Abin da yake so kotu ta yi
A cikin karar, ya roki kotun da ta bayar da umarnin a dakatar masu ruwa da tsakin APC daga shiryawa ko gudanar da taron gangamin na APC a watan Janairu da Fabrairu ko ma a kowace rana ko dai kafin ko bayan sauraron karar da yanke hukunci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan sauraron lauyoyi a kan lamarin, Mai shari’a Bello Kawu ya bayar da umarnin a ranar Juma’a tare da hana jam’iyyar ci gaba da gudanar da taron.
Hakazalika, ya kuma yi gargadin cewa abin da ya shafi shari’ar a yanzu ya zama batun kotu, kuma kada a yi katsalandan a cikinsa.
Tuni dai dama aka shigar da kara a gaban kotu domin nuna rashin amincewa da gudanar da taron gamganmin jam’iyyar na kasa na ranar 26 ga watan Maris.
Mai shigar da karar ya shaida wa kotun cewa:
“Rantsar da kananan kwamitoci na taron gangamin na kasa na ranar 26 ga Maris lokacin da umarnin kotun ke kan batun nuna rashin biyayya ne ga bin doka da oda a kasar.”
Yayin da aka sanya ranar 30 ga Maris, 2022 don ci gaba da sauraron karar, ba a kayyade ranar da za a fara shari’ar matsayar APC ba.
Mai shigar da karar ya kuma yabawa INEC kan yadda ta tsaya kan tanade-tanaden doka da kuma umarnin kotun da ke kan aiki.
A makon da ya gabata ne INEC ta rubutawa APC cewa, ba ta amince da shugabancin gwamnan Neja, Abubakar Sani-Bello ba, sannan ta kuma sanar da APC cewa ba ta yi daya daga cikin sharuddan da ake bukata na gudanar da sahihin taron NEC ko taron gangamin kasa ba.
Wani yanki na wasikar da INEC ta turawa APC da jaridar Blue Print ta ruwaito ya jawo hankalin APC zuwa sashe na 82(1) na dokar zabe wanda ya tanadi cewa:
“Kowace jam’iyyar siyasa da ta yi rajista za ta ba Hukumar sanarwar akalla kwanaki 21 na duk wani taron gangami, majalisa, taro ko taron ganawa da aka shirya domin “hadewa” da zaben mambobin kwamitocinta na zartarwa, sauran hukumomin gwamnati ko nadin ‘yan takara na kowane mukami da aka kayyade a karkashin wannan dokar”.
Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu
A tun farko, Punch ta ce daga cikin karar da aka kai jam’iyyar APC mai mulki a kotu, akwai na yunkurin soke zabukan da aka yi a jihohi da kananan hukumomi.
Masu kalubalantar APC su na ganin tun farko kwamitin CECPC na Mai Mala Buni bai da hurumin shirya zabe a matakin jiha, kananan hukumomi ko ma a mazabu.
Bayanin hadimin shugaban rikon na jam’iyyar APC wanda yanzu aka ce an dakatar daga matsayinsa ya bayyana wannan ne bayan abin da ya biyo baya.
Asali: Legit.ng