Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Tun dawowar mulkin demokradiyya a Najeriya a shekarar 1999, akwai wasu mutane a kasar da suka shiga siyasar aka fara dama wa da su kuma har yanzu suna nan ba su gajiya ba.

Cikin irin wadanda sake dade a siyasar Najeriya suna amfana da kudin gwamnati saboda mukamai da dama da suka rike akwai irinsu Ike Ekweremadu, Ahmad Lawan, Danjuma Goje, David Mark da wasu.

A wannan rubutun, Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin wadannan yan siyasan da suka ka ga jiya kuma sun ga yau kuma da yiwuwar wasunsu za a cigaba da yi da su a gobe.

Ga jerin sunayensu a kasa:

1. Ike Ekweremadu

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999
Sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan majalisa yanzu haka na tarayya, Ike Ekweremadu a ranar Juma’a, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Enugu a 2023. Idan lokacin ya yi, ya yi sanata sau biyar kenan kuma ya kwashe shekaru 20 a matsayin dan majalisa.

Har ila yau, idan zabe mai zuwa yazo kuma ya lashe zaben, Ekweremadu zai kwashe shekaru 26 kenan a mukamai daban-daban na gwamnati kuma ya samu miliyoyin Nairori a matsayin kudin albashi da alawus.

Ya fara siyasa ne a 1997 inda ya zama shugaban karamar hukumar Aninri a karkashin jam’iyyar United Nigeria Congress Party, UNPP, wanda daga nan aka nada shi matsayin shugaban ma’aikata ga gwamnan Jihar Enugu na lokacin, Chimaroke Nnamani, daga 1999 zuwa 2001.

Bayan nan an nada shi a matsayin sakataren gwamnatin Jihar Enugu daga 2001 zuwa 2002 sannan ya fara takarar sanata karkashin jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC

Ya zama sanata a 2003 kuma har yanzu ya ci gaba da rike kujerar inda ake ta zaben shi.

Yayin da ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Enugu, Ekweremadu, wanda lauya ne ya bayyana burin sa na gyara Jihar Enugu.

Sai dai ba shi kadai bane dan siyasa wanda ya kwashe shekarun nan a kan mukamai daban-daban ba.

2. Ahmad Lawan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999
Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan shi ma dan siyasa ne wanda ya kwashe shekaru da dama a kujeru daban-daban.

Tun asali malamin jami’a ne kafin ya koma harkar siyasa. Kuma tun 1999 yake majalisar tarayya, bayan Najeriya ta koma demokradiyya.

Ya fara ne a matsayin dan majalisar wakilai a 1999 inda ya rike mukamin sau biyu har zuwa 2007, daga nan ya koma majalisar dattawa.

Yanzu dai shi ne mutum na uku a Najeriya bayan ya kwashe shekaru 22 yana rike mukamai daban-daban na gwamnati inda yake morar albashi da alawus.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ram da miyagun masu garkuwa da mutane a dajin Kwara

3. Babatunde Fashola

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999
Babatunde Fashola, Ministan Makamashi. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Babban lauyan Najeriya, SAN Babatunde Fashola ya fara siyasa a 1999 a matsayin sakatare na Transitional Work Groups a 1999; kuma mamba ne na Mobaloji Johnson Housing Scheme a Lekki a shekarar 2000.

Mamba ne shi a State Tenders Board, Lagos State Executive Council, State Security Council da State Treasury Board daga shekarar 2002 zuwa 2006.

Daga bisani an nada shi shugaban ma’aikata karkashin mulkin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Jihar Legas har zuwa 2007. Daga nan aka zabe shi a matsayin gwamna har sau biyu inda ya kammala a shekarar 2015.

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nada shi a matsayin ministan a 2015, inda ya ke kulawa da ma’aikatu 3, na ayyuka, wutar lantarki da gidaje.

Yanzu haka minista ne na ma’aikatar ayyuka da gidaje.

A matsayinsa na gwamna, Fashola yana samun fansho da kudade na musamman har yanzu. Ciki har da gidan da zai zauna a ko wanne yanki cikin jihar da kuma gida a Abuja a matsayinsa na wanda ya yi gwamna har sau biyu, sabbin motoci 6 a duk shekara 3, da kuma kaso 100% na albashin sa lokacin yana gwamna, kudin kulawa da lafiyarsa da na iyalinsa, kudin gyaran kujeru da ababen amfani na gida, wanda hakan kaso 300% ne na albashinsa na ko wacce shekara da kuma kudin kula da gidansa da ‘yan sanda 8 da jami’an DSS da za su dinga kulawa da lafiyarsa har ya mutu.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

Sai dai majalisar Jihar Legas ta bayyana batun rage kudin fanshon tsofaffin gwamnoni a watan Augustan 2021 zuwa rabi.

4. David Mark

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999
Sanata David Mark. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma birgediya janar mai murabus, David Mark ya wakilci mazabar Binuwai ta kudu daga 1999 zuwa 2019.

Kafin nan ya rike kujerar gwamnan Jihar Neja a lokacin mulkin soji daga 1984 zuwa 1986 sai kuma ya rike mukamin ministan sadarwa.

Ya so tsayawa takarar shugaban kasa a 2018 inda ya nada Zainab Abdulkadir Kure a matsayin shugaban kamfen din sa da kuma Abba Ejembi a matsayin kakakinsa na bangaren kamfen.

5. Rotimi Amaechi

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999
Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Rotimi Amaechi ya rike kujerar Kakakin majalisar Jihar Ribas na tsawon shekaru 8, tsakani 1999 da 2007.

Bayan nan an zabe shi a matsayin gwamnan jihar inda ya kwashe shekaru 8 a kan mulkin zuwa karshen 2015.

Amaechi ne darekta janar na kungiyar kamfen din Buhari, kuma yana kan kujerar ministan ma’aikatar sufuri a karkashin wannan gwamnatin.

Kara karanta wannan

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

6. Danjuma Goje

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999
Sanata Danjuma Goje. Hoto: Daily Trust

Tsohon gwamnan Jihar Gombe, Danjuma Goje, ya fara siyasa a 1999, lokacin da ya rike kujerar ministan wutar lantarki karkashin mulkin shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Ya zama gwamnan Jihar Gombe a 2003 inda ya kwashe shekaru 8 a mulki.

Har yanzu bai gama ba, ya yi gaggawar wucewa majalisar tarayya a matsayin sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya.

An samu rahotanni akan yadda kusoshi daga mazabar sa suka ki amincewa da ya yi takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164