Daga karshe: Yadda APC ta karkasa kujerun shugabanci a shiyyoyi 6 na kasar nan

Daga karshe: Yadda APC ta karkasa kujerun shugabanci a shiyyoyi 6 na kasar nan

  • Jam'iyyar APC ta shirya gudanar da taronta na gangami a watan Maris dinnan, inda take ci gaba da shiri
  • A yau jam'iyyar ta tura kujerar shugabancinta ga yankin Arewa ta Tsakiya, yayin taron masu ruwa da tsaki
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku jadawalin shugabancin jam'iyyar da kuma inda ta tura kujerun shugabancin na shiyyoyi

FCT, Abuja - A karshe dai kwamitin tsare-tsaren taron gangamin jam'iyyar APC mai mulki ya fitar da tsarin shiyya-shiyya na taron gangaminsa na kasa da za a yi a ranar 26 ga Maris.

Jam’iyyar APC ta ware kujerar shugabancin jam'iyya na kasa zuwa Arewa ta tsakiya yayin da Kudu maso Yamma za ta samar da Sakataren jam'iyya na kasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugabanta na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya

Ofishin mataimakin shugaban jam'iyya na kasa ya tafi ga shiyyar Kudu maso Gabas, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na jam’iyyar, Saliu Na’in a Dambatta ya fitar, an amince da tsarin shiyyoyin ne a taron da kwamtin na CECPC ya yi a ranar 8 ga Maris, 2022, haka nan jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Arewa ta Tsakiya (Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger da Plateau)

1. Shugaban jam'iyya na kasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Arewa Ta Tsakiya).

3. Mataimakin Sakataren jam'iyya na kasa

4. Mataimakin mai ba jam'iyya shawara kan harkokin shari'a na kasa

5. Mataimakin Sakataren Yada Labarai na jam'iyya na Kasa

6. Sakataren jam'iyya shiyya

7. Shugaban Matasan jam'iyya Shiyya

8. Sakataren Tsare-Tsaren jam'iyya na Shiyya

Kara karanta wannan

2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP

9. Shugabar Mata ta jam'iyya ta Shiyya

10. Jagora na Musamman jam'iyya na Shiyya (Nakasassu – PWD)

11. Karin ofishi daya daga yankin

Kudu maso Kudu (Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da Rivers)

1. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Kudu Kudu)

2. Sakataren Yada Labarai na jam'iyya na Kasa

3. Shugabar Mata ta jam'iyya ta Kasa

4. Mataimakin Ma'ajin jam'iyya na Kasa

5. Mataimakin sakataren walwala na jam'iyyar na kasa

6. Sakataren jam'iyya na shiyya

7. Shugaban Matasan na jam'iyya na Shiyya

8. Sakataren Tsare-Tsare na jam'iyya na Shiyya

9. Shugabar Mata ta jam'iyya ta Shiyya

10. Jagora na Musamman jam'iyya na Shiyya (Nakasassu– PWD)

11. Karin ofishi daya daga yankin

Kudu maso Yamma (Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo )

1. Sakataren jam'iyya na kasa

2. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Kudu maso Yamma)

3. Shugaban Matasa na jam'iyya na Kasa

4. Shugaban Nakasassu na jam'iyya na Kasa

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

5. Mataimakin mai binciken kudi na jam'iyya na kasa

6. Sakataren jam'iyya na shiyya

7. Shugaban Matasan jam'iyya na Shiyya

8. Sakataren Tsare-Tsaren jam'iyya na Shiyya

9. Shugabar Matan jam'iyya na Shiyya

10. Jagora na Musamman na jam'iyya na Shiyya (Nakasassu – PWD)

11. Karin ofishi daya daga yankin

Kudu maso Gabas (Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo)

1. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Kudu)

2. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Kudu maso Gabas)

3. Ma'ajin jam'iyya na Kasa

4. Sakataren walwala na jam'iyya na kasa

5. Mataimakin sakataren tsare-tsare na jam'iyya na kasa

6. Sakataren jam'iyyar na shiyya

7. Shugaban Matasan jam'iyya na Shiyya

8. Sakataren Tsare-Tsaren jam'iyya na Shiyya

9. Shugabar Matan jam'iyya na Shiyya

10. Jagora na Musamman na jam'iyya na Shiyya (Nakasassu – PWD)

11. Karin ofishi daya daga yankin

Arewa maso Yamma (Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe)

1. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Arewa)

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

2. Mai binciken kudi na jam'iyya na kasa

3. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (North East).

4. Mataimakin sakataren kudin jam'iyya na kasa

5. Mataimakiyar shugabar mata ta jam'iyya ta kasa

6. Sakataren jam'iyya na shiyya

7. Shugaban Matasan jam'iyya Shiyya

8. Sakataren Tsare-Tsaren jam'iyya na Shiyya

9. Shugabar Matan jam'iyya ta Shiyya

10. Jagora na Musamman na jam'iyya na Shiyya (Nakasassu – PWD)

11. Karin ofishi daya daga yankin

Arewa maso Yamma (Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara)

1. Mataimakin Shugaban jam'iyya na Kasa (Arewa maso Yamma)

2. Mai ba jam'iyya shawara kan harkokin shari'a na kasa

3. Sakataren Tsare-Tsaren jam'iyya na kasa

4. Sakataren Kudin jam'iyya na Kasa

5. Mataimakin shugaban matasan jam'iyya na kasa

6. Sakataren jam'iyya na shiyya

7. Shugaban Matasan jam'iyya na Shiyya

8. Sakataren Tsare-Tsare na jam'iyya na Shiyya

9. Shugabar Matan jam'iyya ta Shiyya

10. Jagora na Musamman na jam'iyya na Shiyya (Nakasassu – PWD)

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar APC ta kasa dake Abuja

11. Karin ofishi daya daga yankin

Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugaba na kasa yankin Arew ata tsakiya

A wani labarin, jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, ta fitar da jadawalin rarraba ofisoshin shugabanninta zuwa yanki-yanki yayin da ranar babban gangamin taro na kasa ke kara matsowa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa APC ta zabi ranar 26 ga watan Maris din nan da muke ciki a matsayin ranar babban taro na kasa, wanda zata zabi mambobin kwamitin zartarwa (NWC) na kasa.

A jadawalin da APC ta fitar yau Laraba a Abuja, jam'iyyar ta mika ofishin shugaban jam'iyya na kasa zuwa yankin arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.