Jerin Shugabannin jam'iyya 4 da aka fitittika daga ofis karfi da yaji

Jerin Shugabannin jam'iyya 4 da aka fitittika daga ofis karfi da yaji

Jam'iyyun siyasar Najeriya mafi adadin mambobi All Progressives Congress APC da Peoples Democratic Party PDP sun fuskanci matsalolin shugabanci a shekarun baya.

Dukkan jam'iyyun biyu sun fitittiki shugabanninsu karfi da yaji a baya.

Ga mutum hudu da aka kora daga kujerunsu:

1. Adams Oshiomole

Adams Oshiomole, wanda ya zama Shugaban jam'iyyar APC a Yunin 2018 ya fara fuskantar matsala lokacin da babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatad da shi ranar 4 ga Maris, 2020.

Alkalin kotun Danlami Senchi, ya bada umurnin korar Oshiomole saboda gundumarsa ta Estako 10 a jihar Edo ta koreshi daga jam'iyyar.

Bayan kai ruwa rana kotuna daban-daban, kotun daukaka kara ranar 16 ga Yuni 2020 ta tabbatar da korar Oshiomole.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

2. Uche Secondus

Secondus wanda ya zama shugaban jam'iyyar PDP a 2017 ya fara samun matsala ne lokacin da wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar suka fara murabus saboda yadda yake tafiyar da mulkinsa.

A ranar 10 ga Satumba, 2021, wata kotun dake Fatakwal ta tabbatar da dakatad da Secondus bayan gundumarsa ta Ward 5, a Andoni jihar Rivers ta koreshi daga jam'iyyar.

Wasu mambobin jam'iyyar ne suka shigar da shi kotu.

Jerin Shugabanni jam'iyya 4 da aka fitittika daga ofis karfi da yaji
Jerin Shugabanni jam'iyya 4 da aka fitittika daga ofis karfi da yaji
Asali: Depositphotos

3. Ali Modu Sherrif

A ranar 16 ga Febrairu Ali Modu Sherrif, wanda tsohon gwamnan jihar Borno ne ya zama mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP.

A ranar 12 ga yuli, 2017, bayan kai ruwa rana kotu tsakaninsa da tsohon gwamnan Kaduna, Ahmad Muhammad Makarfi, kotun koli ta kori Modu Sherrif.

4. Mai Mala Buni

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya zama Shugaban kwamitin rikon kwaryan APC ranar 25 ga Yuni, 2020 bayan rikicin da ya biyo bayan korar Adams Oshiomole.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

Wata shida aka baiwa Buni rikon kwarya amma shekaru biyu har yanzu bai shirya taron gangami ba.

A ranar 7 ga Maris, 2022, rahotanni sun nuna cewa Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni kuma Gwamnan Neja ya maye gurbinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng