Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta amince da rahoton kwamitin tsarin mulkin karba-karba
- Jam'iyyar APC ta ƙasa ta amince da rahoton kwamitin rarraba mukamai bisa jagorancin gwamnan Kwara
- Shugaban rikon kwarya na APC ta kasa, gwamna Abubakar Bello na Neja, shi ne ya faɗi haka a Abuja
- Rikicin cikin gida na cigaba da ƙara ruruwa a APC, yayin da rahoto ke nuna cewa an samu canjin shugaban rikon kwarya
Abuja - Shugaban rikon kwarya na APC ta ƙasa kuma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, yace jam'iyya ta amince da rahoton kwamitin kasafta kujeru da ta karba.
Channels TV ta rahoto Gwamna Bello na cewa APC ta amince da rahoton wanda ta karba daga shugaban Kwamitin, kuma gwamnan Kwara, Abdullrahman Abdulrazak, kuma za'a sake shi anjima.
Ya kuma kara da cewa mako mai zuwa jam'iyyar APC zata gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai halarta daga inda yake.
A ranar Litinin ta makon da ya gabata ne, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da ɗage babban taronta na ƙasa zuwa ranar 26 ga watan Maris, 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun da farko ta tsara gudanar da babban taron a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022, amma saboda rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa da kuma darewar jam'iyyar a wasu matakai ya jawo jinkiri.
Da yake martani kan rahoton rabuwar APC, gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya ce:
"Babu ta yadda zaka haɗa gwamnoni 22 kuma kace komai ra'ayinsu ya zo ɗaya. Dole wataran a samu banbancin ra'ayi, amna a kira shi da rabuwar kai ya yi nisa."
Wane rikici APC ta tsinci kanta?
Yayin da raɗe-raɗin wutar rikici a cikin APC ta kara yawaita, ba zato a ranar 7 ga watan Maris, sabon labari ya bulla cewa akwai yuwuwar an tsige shugaban rikon kwarya, gwamna Mala Buni.
Wannan ya biyo bayan kalaman gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, cewa shi ne shugaban rikon kwarya kuma ya jagoranci taron kwamitin rikon kwarya a Abuja.
A wani labarin kuma Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP
Wasu kusoshin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Rano ta jihar Kano sun yi murabus daga kan mukamansu da nufin bin Kwankwaso.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai bar PDP kafin karshen watan Maris, alamu sun nuna zai koma NNPP.
Asali: Legit.ng