Da dumi-dumi: Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja

Da dumi-dumi: Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja

  • Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya ce ya dauki tsawon lokaci rike da mukamin mukaddashin shugaban APC na kasa
  • Bello ya bayyana hakan ne a sakatariyar jam'iyyar mai mulki da ke Abuja bayan ya jagoranci wani taron kwamitin rikon
  • Ya ce tun bayan da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tafiya, shine ke jan ragamar iko na jam'iyyar

Abuja - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa an dan dauki tsawon lokaci yanzu da ya fara aiki a matsayin shugaban riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa.

Bello ya fadi hakan ne a ranar Litinin, 7 ga watan Maris, bayan ya jagoranci wani taron kwamitin riko na jam’iyyar ta kasa, a sakatariyar APC da ke Abuja, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Da dumi-dumi: Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja
Gwamnan Neja ya ce tun bayan tafiyar da Buni ya yi, shine ke jagoranci a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC Hoto: @abusbello
Asali: Twitter

Tunda Mala Buni ya yi tafiya nake jagoranci - Gwamna Bello

Vanguard ta rahoto cewa da aka tambaye shi kan ko a wani mizani ya karbi ragamar kula da jam’iyyar, sai gwamnan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mukaddashin shugaba, na dade ina rike da mukamin tunda shugaban rikon ya yi tafiya."

Rahoton ya kuma kawo cewa da aka matsa masa domin ci gaba da yin bayani, sai ya ce: “Babu sharhi.”

Gwamnan Neja ya dira hedkwatar APC don maye gurbin Mai Mala Buni

Mun kawo a baya cewa Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, wanda aka fi sani da Abu-Lolo ya dira hedkwatar uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC don maye kujerar kwamitin rikon kwarya.

Rahoton TVCNews ya biyo bayan kulle hedkwatar da jami'a yan sanda suka yi.

Dirarsa ya tabbatar da labarin cewa da alamun mulkin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, matsayin shugaban jam'iyyar ya zo karshe.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng