Yanzu-Yanzu: Gwamnan Neja ya dira hedkwatar APC don maye gurbin Mai Mala Buni

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Neja ya dira hedkwatar APC don maye gurbin Mai Mala Buni

  • Rikicin APC ya dau sabon salo yayinda ake rade-radin cire shugaban jam'iyya Mai Mala Buni
  • Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin cire Gwamnan na Yobe
  • A madadinsa, an ce an nada Gwamnan jihar Neja ya samu sabon shugaban jam'iyyar

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, wanda aka fi sani da Abu-Lolo ya dira hedkwatar uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC don maye kujerar kwamitin rikon kwarya.

Rahoton TVCNews ya biyo bayan kulle hedkwatar da jami'a yan sanda suka yi.

Dirarsa ya tabbatar da labarin cewa da alamun mulkin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, matsayin shugaban jam'iyyar ya zo karshe.

Wannan sabon canji na zuwa ne ana saura yan makonni taron gangamin jam'iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren Kwamitin, John AkpanUdoedehe, hakazalika ya dira hedkwatar ta kasa.

Shugabannin jam'iyyar yanzu haka sun shiga ganawar sirri da Gwamnan jihar Nejan.

Gwamnan Neja
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Neja ya dira hedkwatar APC don maye gurbin Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel