Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara
- Kungiyar matasan APC a arewa sun marawa takarar Gwamna David Umahi baya don ganin ya zama shugaban kasa a 2023
- A yanzu haka, kungiyar kammala tsare-tsare domin siya masa tikitin yin takarar
- Matasan sun kuma jadadda cewar Umahi ne ya cancanci maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin daurawa daga inda ya tsaya
Kungiyar matasan APC a arewa sun jadadda jajircewarsu don ganin David Nweze Umahi ya zama shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.
Kungiyar ta hannun shugabanta, Hon. Suleiman Liba, ta kuma bayyana cewa domin tabbatar da hakan, sun kammala tsare-tsare domin siyawa gwamnan tikitin takarar shugaban kasa na APC, Vanguard ta rahoto.
Hon. Liba, a cikin wata sanarwa, ya roki dukkan masu ruwa da tsaki da masu niyan yin takarar shugaban kasa, musamman wadanda suka fito daga yankin kudu maso gabas da su hadu sannan su marawa takarar Dave Umahi baya.
Vanguard ta nakalto Liba yana cewa:
“Kasancewar shi ke da babban dama ba wai a tsakanin yan takarar APC ba kawai harma a kasar gaba daya.
“Hakan ya samo asali ne saboda irin nasarorin da ya samu a baya da kuma goyon bayan da Umahi ya samu a duk fadin kasar a cikin 'yan shekarun nan.
“Kungiyar ta matasan APC a arewa ta kammala shirye-shirye domin yin gangamin mutane miliyan daya a fadin jihohin arewacin Najeriya domin nuna goyon baya ga Umahi.”
Kungiyar ta ci gaba da cewa:
“Wannan ba don mutum daya bane illa don ra’ayin dukkaninmu da kasar gaba daya.
“Ya zama dole a ci gaba da kyakkyawar manufar shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma mutumin da ya cancanci ci gaba da hakan ba kowa bane face Mai girma, Injiniya David Nweze Umahi.”
Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam
A wani labarin, shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Nasarawa, Dr Kassim Muhammed Kassim, ya bayyana cewa sun tara naira miliyan 10 domin siyawa Sanata Abdullahi Adamu tikitin takara.
Kassim ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki daga yankin arewa ta tsakiya ne suka hada kudin, Daily Trust ta rahoto.
Tsohon gwamnan na jihar Nasarawa yana hararar kujerar shugaban APC na kasa a babban taron jam’iyyar mai zuwa.
Asali: Legit.ng