Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

  • Magoya baya sun hada kudi har naira miliyan 10 domin siyawa Abdullahi Adamu tikitin takarar kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa
  • Masu ruwa da tsaki na APC a arewa ta tsakiya ne suka hada kudin kamar yadda jigon jam'iyyar a jihar Nasarawa, Dr Kassim Muhammed Kassim, ya bayyana
  • Adamu dai shine zabin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan kujera

Nasarawa - Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Nasarawa, Dr Kassim Muhammed Kassim, ya bayyana cewa sun tara naira miliyan 10 domin siyawa Sanata Abdullahi Adamu tikitin takara.

Kassim ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki daga yankin arewa ta tsakiya ne suka hada kudin, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam
Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Nasarawa yana hararar kujerar shugaban APC na kasa a babban taron jam’iyyar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Saraki: Yadda kura-kuran PDP ya kawo Buhari kan karagar mulki

An tattaro cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lamunce masa a matsayin dan takarar da yake goyawa baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abun da yasa muka hada kudin siya masa fam - Kassim

Kassim ya fada ma manema labarai a Lafia cewa dalilin da ya sa suka tara kudin shi ne don nuna goyon baya ga Adamu da kuma gode masa kan kafa manyan makarantu da ya yi a jihar a lokacin da yake gwamna, wanda hakan ya ba su damar samun ilimi mai zurfi.

Ya bukaci wadanda ke ikirarin cewa su magoya bayan shugaban kasar ne sannan suke adawa da zabinsa da su sake tunani.

Ya ce:

“Ba zai yiwu ku dunga fada ma yan Najeriya cewa kuna son Buhari ba sannan ku juya baya don yin adawa da hukuncinsa, ya fito fili sannan wannan ne dalilin da yasa Buhari ya fadi zabe a wasu jihohin.”

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

Hakazalika Dr Kassim ya nuna rashin jin dadinsa da yadda wasu matasa suka mika kansu wajen yiwa Adamu zagon kasa da zarge-zarge marasa tushe, wadanda a cewarsa suna da rauni ga dimokaradiyyar mu, rahoton Vanguard.

Magana ta kare: Buhari ya tsaida wanda yake so ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC

A baya mun ji cewa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince tsohon gwamna, Abdullahi Adamu ya karbi rikon jam’iyya.

Wata majiya mai karfi har daga fadar wasu gwamnoni ta shaidawa Daily Trust cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya nuna yana tare da Sanata Adamu.

Shugaban kasar ya nuna inda ya karkata ne a wajen taron da ya yi da gwamnonin APC a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng