Obasanjo: Galibin Masu Son Zama Shugaban Ƙasa Ya Kamata Suna Ɗaure a Gidan Yari

Obasanjo: Galibin Masu Son Zama Shugaban Ƙasa Ya Kamata Suna Ɗaure a Gidan Yari

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce akwai ‘yan takarar shugaban kasa na 2023 da dama da suka cancanci zaman gidan yari da EFCC da ICPC sun yi ayyukan da suka dace su yi
  • Ya yi wannan furucin ne a ranar Asabar yayin wani taro na kasa da kasa da aka shirya musamman don bikin murnar cikar sa shekaru 85 da haihuwa a OOPL da ke Abeokuta, Jihar Ogun
  • Ya ce hakan ne babban dalilin da ya hana shi mara wa ko wanne dan takarar da ya kai masa ziyara baya, don neman goyon bayan sa wurin zawarcin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da ke karatowa

Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce akwai ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da suka cancanci zaman gidan yari da hukumar yaki da rashawa, EFCC ta yi aikin da ya dace, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Saraki: Yadda kura-kuran PDP ya kawo Buhari kan karagar mulki

Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin wani taro na kasa da kasa da aka shirya don bikin zagayowar ranar haihuwar sa ta 85 wanda aka yi a Olusegun Obasanjo Presidential Library, OOPL, da ke Abeokuta a cikin Jihar Ogun inda yace akwai gurbatattu a cikin ‘yan takarar.

Obasanjo: Galibin Masu Son Zama Shugaban Ƙasa Ya Kamata Suna Ɗaure a Gidan Yari
Galibin Masu Son Zama Shugaban Ƙasa Ya Kamata Suna Ɗaure a Gidan Yari Idan Da ICPC Da EFCC Na Aikinsu Yadda Ya Kamata. Hoto: Femi Adesina
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obasanjo wanda ya yi wa jawabin nasa take da ‘Labarin Afirka da halin da Najeriya take ciki’, ya ce ‘yan takarar shugaban kasa a 2023 da dama sun ziyarce shi amma har yanzu bai mara wa ko mutum daya baya ba.

Dalilin sa na kin mara musu baya

Tsohon shugaban kasar ya kada baki ya ce:

“Ina ta kallon yadda ‘yan takara suke ta kai komo. Da kamar EFCC da ICPC sun yi ayyukan su bisa ka’ida kuma shari’a ta taimaka musu yadda ya dace, da yanzu yawancin su suna gidan yari.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari Ya Ce Yana Shawara Domin Fitowa Takarar Kujerar Shugaban Kasa

“Duk mutumin da ba ya da gaskiya bai cancanci a amince masa ba. Wajibi ne a bi hanyar da ta dace wurin gyara Najeriya ba tare da daga kafa ba, kawaici, sanya bangaranci, rashin adalci, sanya batun addini, dubi da arziki ko kuma matsayi.
“Wajibi ne a samar da tsaro, ci gaba, kwanciyar hankali, tattalin arzikin kuma agyara alakar mu a cikin nahiyar Afirka da sauran bangarori na duniya in har ana so kasa ta ci gaba.
“Ya kamata mu yi koyi da abubuwan da suka auku a kusan shekaru 24 da suka gabata, dole mu yarda da cewa mu ne ba mu yi aiki na kwarai ba, ba mu dinga cewa Ubangiji ne ya daura mana ba.”

Kamar yadda Vanguard ta rahoto , ya ci gaba da horar ‘yan Najeriya da zaben mutanen kirki kuma masu tsoron Allah. Ya bukaci a zabi wadanda zasu yi ayyuka na kwarai don samar da ci gaba.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Ya bayar da misalin yadda aka cire bangaranci a shekarun baya

Ya bayar da misali akan yadda aka zabi Shehu Shagari a shekarar 1979 da Alex Ekwueme daga Biafra a matsayin mutum na biyu a kasa cikin kasa da shekaru 10 da yunkurin raba Biafra wanda hakan ya janyo hadin kai a kasa.

A cewarsa ‘yan Najeriya sun zabe shi a 1999 lokacin da Afenifere da sauran yarabawa suka ki zaben shi wanda hakan ya kara janyo hadin kai a kasa.

Ya ce Umaru Yar’Adua ya amshi mulki bayan shi, wanda dan arewa ne, kuma lokacin da ya rasu yana kan kujerar mulki, Jonathan ya gaje shi kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Idan binciko laifuka za a yi, kowa ba zai sha ba

Ya ci gaba da cewa idan aka ci gaba da neman laifin yankuna ko addinai, babu yanki ko addinin da ba za a kama da laifi ba. Don haka wajibi ne gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wurin bunkasa kasa tare da hada kan ‘yan kasar.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Atiku Ya Kai Wa Obasanjo Ziyara a Gida, Sun Keɓe Suna Ganawar Sirri

Ya ci gaba da cewa lokaci ya yi da Najeriya zata zabi nasara daga rashin ta, ta kuma hada kai da ko wanne yanki wurin ganin ta dawo daidai, kamar yadda take a da ko kuma fiye da hakan.

Daga karshe ya yi wa kasar fatan alheri da kuma fatan samun ci gaba mara misaltuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164