2023: Shehu Sani Ya Bayyana Abin Da Zai Yi A Kaduna Idan An Zabe Shi Gwamna

2023: Shehu Sani Ya Bayyana Abin Da Zai Yi A Kaduna Idan An Zabe Shi Gwamna

  • Mai neman takarar gwamnan Jihar Kaduna a jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani, ya yi akawarin zama gada tsakanin mutanen Arewacin Kaduna da Kudancin jihar idan aka zabe shi a matsayin gwamna a 2023
  • Sani ya sha wannan alwashin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a inda ya ce jihar tana bukatar shugaban da zai kawo hadin kai, adalci da daidaito a fadin ta
  • Hakan yasa ya bukaci goyon baya da addu’o’i daga mutanen kudancin Kaduna don ya samu nasarar zama gwamna kuma ya yi akawarin zai ba kowa dama don a dama da shi

Kaduna - Dan takarar gwamna a Jihar Kaduna jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani, ya yi alkawarin samar da shugabancin da zai zama gada tsakanin arewa da kudancin Jihar Kaduna idan ya zama gwamna a 2023, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Sani ya bayyana wannan kudirin nashi ne a ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a.

2023: Shehu Sani Ya Bayyana Abin Da Zai Yi A Kaduna Idan An Zabe Shi Gwamna
2023: Shehu Sani Ya Zai Hada Kan Arewa Da Kudancin Kaduna Idan An Zabe Shi Gwamna. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Kamar yadda ya ce, Kaduna tana bukatar shugaba wanda zai kawo hadin kai ga jama’a da kuma adalci da daidaito tsakanin su.

Shehu Sani ya ce zai kawo hadin kai a jihar

Ya ce:

“Mutanen Jihar Kaduna suna bukatar shugaba wanda zai kawo hadin kai tsakanin su don gudun rabuwar kawuna.
“Abinda muke bukata shi ne hadin kai da tsaro a tsakanin mutanen mu da kuma shugaba adali. Zan samar da shugabanci wanda zai kawo ci gaba a cikin kananan hukumomi 23 da ke jihar.”

Ya bukaci hadin kai da addu’o’in mutanen kudancin Kaduna don ya samu nasara wurin ba kowa dama don a dama da shi kamar yadda The Punch ta nuna.

Kara karanta wannan

Abin da PDP za tayi kafin tayi nasara a zabe - Gwamna Tambuwal ya bada lakanin 2023

Ya shaida cewa:

“Na dade ina iyakar kokari na akan mutanen kudancin Kaduna. Na dade ina tsaya wa mutanen Jihar Kaduna.
“Don haka na zo nan ne don neman hadin kan jama’an kudancin Kaduna akan buri na na takarar gwamna don kawo hadin kai, tsaro da ci gaban Jihar Kaduna.
“Na zo ne don neman hadin kan ku da addu’o’i gami da goyon baya.”

Sani ya ce PDP ce kadai zata iya samar da tsaro a jihar

Yayin da aka tambaye shi idan har akwai yuwuwar PDP ta lashe zaben gwamna a shekarar 2023, ya ce rashin tsaron da ya yawaita yayin da APC take shugabanci kadai ya isa ya sa a zabi PDP.

Mutanen Jihar Kaduna ba su da wani zabin da ya wuce su yi jam’iyyar PDP saboda APC ta kasa tsare rayuka da dukiyoyin mutane, a cewarsa.

“Ana halaka mutanen mu tare da garkuwa da wasu. Mutanen kauye sai sun biya kudin haraji sannan suke iya zuwa gonaki don girbin shukokin su.”

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Ya ce dalibai kansu yanzu basu da kwanciyar hankali yayin zuwa makaranta saboda tsoron ‘yan bindiga su halaka su ko kuma su sace su.

Ya kara da cewa PDP ce kadai jam’iyyar da zata kawar da barna da rashin tsaro tare da samar da adalci a fadin Jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164