'Karin Bayani: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich

'Karin Bayani: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich

  • Roman Abramovich, mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ya tabbatar da cewa ya saka kungiyar a kasuwa bayan Rasha afka wa Ukraine da yaki.
  • Biloniyan dan kasar Rasha, ya ce ya dauki matakin sayar da Chelsea ne don ya yi imanin hakan ne alheri ga kungiyar a yanzu kuma zai bada kudin ga mutanen da yaki ya ritsa da su a Ukraine
  • Akwai hasashen cewa Burtaniya za ta iya saka wa Abramovich takunkumi da yiwuwar kwace kungiyar ta Chelsea hakan na iya zama dalilin da yasa ya saka kungiyar a kasuwa a yanzu

Mai kungiyar kwallon kafa na Chelsea, Roman Abramovich, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa zai sayar da kungiyar ta Firimiya League yayin da Rasha ta kutsa Ukraine, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda jariri mai watanni 19 ya fada rijiya, ya nutse a jihar Kano

Biloniyan dan kasar Rasha, Abramovich, ya ce 'zai fi alheri' idan ya rabu da kungiyar da ya sauya ta tun bayan da ya siye ta a shekarar 2003.

Da Ɗumi-Ɗumi: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich
Abramovich: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abramovich ya ce:

"Kamar yadda na ce a baya, duk matakan da na ke dauka wadanda za su fi zama alheri ne ga kungiyar."
"A halin da ake ciki yanzu, na yanke shawarar in sayar da kungiuar, domin ina ganin hakan shine alheri ga kungiyar, yan wasan, masoyansu, masu aiki da masu daukan nauyi da abokan hulda."

Akwai yiwuwar Burtaniya na iya saka wa Abramovich takunkumi don kusancinsa da Putin

Gwamnatin Birtaniya kawo yanzu bata saka wa Abramovich takunkumi ba, kasancewa ana ganin na hannun daman Vladimir Putin ne, amma mai kungiyar na Chelsea ya fargabar kwace kungiyar hakan ya saka a kasuwa.

Kara karanta wannan

Duk za mu mutu: Yaro ya fashe da kuka, yana tsoron ka da Rasha ta harbo bam Najeriya

Rahotanni sun ce biloniya dan kasar Switzerland Hansjorg Wyss da Mai saka hannun jari na Amurka, Todd Boehly ne suke shirin fara tayin siyan kungiyar.

Abramovich, wanda a baya-bayan nan ya tafi ya kalli wasan Chelsea a Abu Dhabi, ya yi alkawarin zai bada kudin da ya siyar da kungiyar domin tallafawa wadanda yaki ya ritsa da su a Ukraine.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164