Mun yi ittifaki, Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN
- Kungiyar CAN ta bayyanawa kasashen Turai cewa adalci shine Kirista dan kudu ya hau kujeran Buhari a 2023
- Shugaban CAN yace tunda Buhari Musulmi ne kuma dan Arewa, ya kamata kujerar ta sauya zani
- Gamayyar kasashen Turai EU ta iso Najeriya don bincike kan shirye-shiryen da akewa zaben 2023
Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta bayyana cewa ta yi ittifaki kuma ta yanke shawara kan matsayarta game da zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
Shugaban CAN na kasa, Rabaran Samson Ayokule yace wajibi ne Shugaban kasa na gaba ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya.
A cewarsa, CAN ba tada wani dan takara amma ba zata taba yarda Musulmi da Musulmi suyi takara ba.
Ayokunle yace:
"Ko da kundin tsarin mulki bai yi maganan tsarin kama-kama tsakanin yankunan Najeriya shida ba, ya kamata jam'iyyun siyasa su hankalta ta hanyar yin kama-kama."
"Mun gargadi dukkan jam'iyyun siyasa kada su kuskura su baiwa Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista tikiti."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Tun da Shugaba Muhammadu Buhari Musulmi ne daga Arewa, toh idan za'ayi adalci da daidaito da hadin kai, a baiwa Kirista daga kudu shugaban kasa."
Ayokunle ya bayyana hakan ranar Talata a hira da wakilan gamayyar kasashen turai EU karkashin jagorancin mai lura da zabe na EU, Ms Maria Arena, rahoton TheNation.
Tawagar EU ta gana da kungiyar CAN don sanin matsayarta kan shirye-shiryen da hukumar zabe INEC, jami'an tsaro da jam'iyyun siyasa ke yiwa zaben 2023.
Mu zamu sake zaban wanda zai zama Gwamna a Taraba: Kungiyar CAN ta caccaki Musulmai
A wani labarin kuwa, Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN a jihar Taraba ranar Alhamis ta bayyana cewa ita zata sake zaban wanda zai zama gwamnan Taraba saboda yawan mabiyanta.
Kungiyar ta caccaki majalisar Musulman jihar Taraba da kungiyar kare hakkin Musulmai MURIC bisa ikirarin da suke na cewa ana musgunawa Musulmai a jihar.
CAN tace ko Musulmai su yarda ko kada su yarda sune maras rinjaye a jihar kuma ba zasu taba nasara a zabe ba.
Asali: Legit.ng