Dokar zabe: Yadda Gwamnatin Jonathan ta so bankara doka domin hana Buhari mulki

Dokar zabe: Yadda Gwamnatin Jonathan ta so bankara doka domin hana Buhari mulki

  • Fadar shugaban kasa ta zargi Goodluck Jonathan da kokarin ganin PDP ta cigaba da mulki a 2015
  • Garba Shehu ya bayyana cewa Gwamnatin PDP ta yi yunkurin ganin Buhari bai yi nasara a zabe ba
  • Hadimin shugaban kasar ya yi bayanin hikimar da ta sa aka rattaba hannu a kudirin gyaran zabe

Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi bayanin yadda gwamnatin Goodluck Jonathan tayi kokarin ganin ta hana Muhammadu Buhari samun nasara a zaben 2015.

Punch ta rahoto Garba Shehu yana wannan bayani bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran zabe na 2022 wanda ya zama doka.

Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi na musamman da ya yi wa take da ‘Assent into law of the electoral act 2022: Landmark moment for the nation’ a jiya.

Kara karanta wannan

Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

Shehu ya ce rattaba hannu da Mai gidansa ya yi a kan wannan kudiri babban nasara ce ga al’umma.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa a lokacin da Goodluck Jonathan yake kan mulki, ya yi duk abin da zai iya wajen ganin PDP ba ta sauka daga mulki ba.

Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Garba Shehu

“Babu wahala a manta da cewa zaben 2015 shi ne karon farko a tarihin Najeriya da aka canza shugabanni ta akwatin zabe, karon farko da wani ‘dan takaran da ya fito daga wajen jam’iyyar PDP da ke mulki ya samu nasara tun da aka dawo farar hula.”
“An yi wannan ne duk da wancan gwamnatin tayi duk abin da za ta iya wajen ganin ta bankara dokar zabe domin ta cigaba da mulki bayan tsawon shekaru 16.” - Garba Shehu.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Buhari ta ke kokarin tsawaita wa’adinta har bayan 2023 inji PDP

Garba Shehu ya kawo yadda Muhammadu Buhari ya sake samun nasara a zaben 2019 da ratar kuri’a kusan miliyan hudu, wanda ya ba shi damar ya zarce a mulki.

Amfanin dokar kasa

Duk da Buhari da APC sun samu kuri’u miliyan 15 a zaben da ya wuce, Malam Shehu ya ce gwamnati ba ta manta da bukatar gyara dokokin zaben Najeriya ba.

Matsalolin da ake samu a wajen zabe ya tunzura shugaban kasa wajen sa hannu a kudirin gyaran zabe na 2022, bayan an ta kai ruwa-rana tsakaninsa da 'yan majalisa.

Hadimin ya ce dokar za ta tabbatar da zabe mai inganci, ta ba jam’iyyu da ‘yan takara damar gwabzawa, sannan kuma za ta takaita siyasar kudi da kuma banga.

Atiku zai kai labari?

Kassim Afegbua wanda ya taba zama mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar ya juya masa baya a wannan karo inda ya ce bai kamata a sake ba Atiku tikiti ba.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Tsohon Hadimin na Atiku Abubakar ya ce bai kamata PDP ta yi wani gigin tsaida shi takara a 2023 ba, ganin yadda ya yi watsi da su bayan ya sha kashi a 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng