Muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da Mahdi Aliyu da Majalisa ta tsige a Zamfara
- A yau Laraba, 23 ga watan Fabrairu, 2022, majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau
- Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC, alaƙa tai tsami tsakanin su, mun tattaro muku abu hudu game da Gusau
- Gusau babban masoyin jam'iyyar PDP ne kuma ɗa ne ga tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Aliyu Gusau
Zamfara - A ranar Laraba, majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Barista Mahdi Aliyu Gusau, daga kan kujerarsa.
Daily Trsut ta rahoto cewa Gusau ya jima yana fafutukar rike mukaminsa tun bayan sauya shekar gwamna Bello Matawalle daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Duk da tun farko hukumar zaɓe INEC ta sanar da abokan takararsu ne suka lashe zaɓen, amma Kotun koli ta yanke hukuncin da ya ba su Nasara awanni kaɗan kafin rantsarwa.
Hukuncin Kotun Allah ya isa ya kwace baki ɗaya kujerun da jam'iyyar APC ta lashe, ya mika wa abokan hamayyar su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wannan labarin, Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da tsohon mataimakin gwamnan.
1. Kafa tarihin zama matashin mataimakin gwamna
An haife shi a ranar 5 ga watan Disamba, 1981, Gusau, kafin yau, shi ne matashi mafi karancin shekaru da ya zama mataimakin gwamna a irin siyasar Najeriya ta wannan lokacin.
Fitaccen ɗan siyasan, wanda ke magana cikin natsuwa da sanin kalaman da zai faɗa, ya zama jagoram PDP a Zamfara, bayan ficewar gwamna Bello Matawalle a watan Yuni, 2021
2. Yana da shekara 32 ya nemi takarar ɗan majalisar tarayya
Zaɓen 2019 ba shi ne karo na farko da Mahdi Gusau ya nemi takara kuma ya sha ƙasa ba, duk da Kotu ta yi hukunci mai kyau a gare sa, zamu ce ya ci sa'a da bai samu nasara ba lokacin yana shekara 32.
Barista Gusau ya nemi takarar ɗan majalisar dokokin tarayya a shekarar 2015 karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
3. Ɗan a mutun PDP
Kasancewarsa ɗan a mutum PDP ne ya yi awon gaba da kujerarsa domin shi kansa Gusau ya amince da haka lokacin da ya yi tsokaci kan shirin tsige shi a karshen mako.
Ya ce duk wannan zargin da ake jefa masa zai kau inda ace ya sauya sheka zuwa APC kamar yadda Matawalle ya yi.
A jawabinsa ya ce:
"Abin da suke nufi a fili yake. Na aje makamai na, na koma jam'iyyarsu ta APC, daga nan komai zai wuce. Shin akwai gaskiya a zargin da suke mun kenan? Suna son cika burin su ne, amma ni ba haka nike ba."
4. Ya fito daga tsatsan Janar ɗin Sojoji
Mataimakin gwamnan da aka tsige ba tantama ya biyo bayan tarihin rashin tsoro na mahaifinsa Janar Aliyu Gusau Mai Ritaya.
Innalillahi: An bindige shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta a cikin gida, Allah ya masa rasuwa
Girmama wa a wani fanni, rashin tsoro, Janar Aliyu ya rike manyan ofisoshi. Ya yi aikin mai bada shawara kan harkokin tsaro ga shugaban ƙasa uku a Najeriya.
Haka nan ya zama shugaban rundunar sojojin kasan Najeriya a zamanin mulkin Ernest Shonekan, da kuma farkon mulkin Sani Abacha.
Ya rike shugabancin hukumomin tsaro daban-daban kuma ya rike kwamanda a makarantar sojoji Nigerian Defence Academy.
Duk da a yanzun ba ya tsoma hannu a abubuwan da suka shafi siyasa, Janar Gusau na da matukar girma a wurin jam'iyyar hamayya PDP.
A wani labarin na daban kuma Kotu ta bada umarnin kwace kadarori 10, da kudaden Banki na tsohon gwamnan Zamfara
Kotun tarayya a Abuja ta ba da izinin kwace kadarori kusan 10 da makudan kudin dake kwance a Banki mallakin Abdul'aziz Yari.
Alkalin Kotun ya ce umarnin na wucin gadi zai kwashe kwanaki 60, kuma bayan haka ICPC zata iya neman kwace su har abada.
Asali: Legit.ng