2023: Idan Baka Fito Takara Ba, Za Mu Ɗauke Ka Rago Kuma Matsoraci, Ƙungiya Ga Atiku

2023: Idan Baka Fito Takara Ba, Za Mu Ɗauke Ka Rago Kuma Matsoraci, Ƙungiya Ga Atiku

  • Dangane da zaben 2023 da ke karatowa, matasan wasu yankuna na kudu sun bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa
  • Kungiyar ta hadin kan matasan kudu, SOYA ta ce idan har Atiku bai bayyana kudirinsa na takara yanzu ba, zata fassara hakan a matsayin tsoro ko rashin jarumta
  • Shugaban SOYA, Ismail Ridwan ya yi wannan furucin a Abeokuta, Jihar Ogun a ranar Litinin yayin taron tattaunawa da manema labarai wanda reshen kungiyar na kudu maso yamma masu goyon bayan Atiku ta shirya

Ogun - Matasan kudancin Najeriya sun huro wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wuta akan kin bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke karatowa.

2023: Ka Fito Ka Bayyana Ƙudirinka Na Takarar Shugaban Ƙasa, Ƙungiya Ga Atiku
2023: Kungiya ta bukaci Atiku ya fito takarar shugabancin kasa. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

The Punch ta rahoto cewa matasan da ke karkashin kungiyar hadin kan matasan kudu, SOYA sun nemi ya fito fili ya bayyana kudirinsa ko kuma su fassara shirunsa a matsayin tsoro.

Kara karanta wannan

2023: Matasa a yankin Kudu sun nace, sun nemi Atiku ya bayyana kudurinsa na takara

Shugaban SOYA, Ismail Ridwan, yayi wannan furucin a Abeokuta, Jihar Ogun a ranar Litinin yayin wani taro na manema labarai wanda ‘yan kungiyar na kudu maso yamma suka shirya don goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar.

Kungiyar ta ce Atiku ne zai iya hada kan kudu da arewacin Najeriya

Mambobin kungiyar sun rike takardu wadanda aka rubuta ‘Shekaru fa’ida ne ga Atiku’, ‘Atiku yana son matasa’, ‘Atiku zai rike PDP da kyau,’ ‘Sai Atiku ya yi shugaban kasa a 2023,’ da sauran su duk da harshen turanci.

Shugaban SOYA ya kula da yadda kungiyar sa ta samar da gurbin shugabanci ga matasa inda ya ce ya kamata a fi mayar da hankali akan shugabanni nagari.

Ya bayyana matsalolin da Najeriya take fuskanta wanda ya ce ciki har da fatara, rashin tsaro, basuka, da sauran su inda ya ce ya kamata Najeriya ta samu shugaba wanda zai fito fili ya fadi gaskiya kuma ya hada kan kudu da arewa

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Saraki ya cancanci darewa kujerar Buhari, in ji kungiyar matasa

A cewar Ridwan, kamar yadda The Punch ta rahoto ta bayyana, Atiku yana da duk halayen da ake bukata wurin shugaban da zai gyara matsalolin Najeriya kuma ya daidaita kasar.

Ya ce:

"Ba mu gamsu da shiru da jan kafa da Atiku ke yi na bayyana niyarsa na yin takarar shugaban kasa ba.
"Idan bai fito ba, za mu dauka cewa shi rago ne; za mu gane dauka ya ji tsoro."

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164