Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage gangamin taronta na ƙasa

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage gangamin taronta na ƙasa

  • Jam'iyya mai mulkin kasar nan APC ta sanar da ranar da zata gudanar da zaɓen shugabanninta na shiyyoyin Najeriya
  • APC ta ɗage babban taron ƙasa, amma ba ta sanar da sabuwar rana ba a wata wasika da ta sake aike wa hukumar zaɓe INEC
  • Rikicin APC reshen jihohi da kuma gaza cimma matsaya kan raba kujerun kasa na daga cikin abubuwan da suka takura wa APC

Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulkin Najeriya ta ɗage babban taronta na ƙasa har sai baba ta gani, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Tun farko dai APC ta tsara gudanar da taron a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022, amma lamarin raba kujerun shugabanni zuwa yanki-yanki da kuma rikici a wasu jihohi suka hana jam'iyyar motsa wa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja

Tutar APC
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage gangamin taronta na ƙasa Hoto: Muaz Magaji/Facebook
Asali: Facebook

A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 21 ga watan Fabrairu, 2022, kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa ya sanar da hukumar zaɓe INEC cigaban da aka samu.

Wasikar da Jam'iyyar ta aike wa INEC na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mala Buni da Sakatarensa, Sanata John James Akpanudoedehe.

Me ke kunshe a wasikar APC?

A wasikar da Legit.ng Hausa ta gani, APC ta ce:

"Wannan sanarwan ta zarce ranar da muka saka a takarda mai lamba APC/NHDQ/INEC/019/22/14. Matakin ya yi dai-dai da kwansutushin ɗin jam'iyyar mu."
"Bisa biyayya ga dokokin kwansutushin, muna mai sanar da hukumar INEC cewa jam'iyyar mu mai albarka APC ta shirya gudanar da babban taron shiyyoyi ranar 26 ga watan Maris, 2022."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Koma Wa Aso Rock

"Muna fatan zaku shirya jami'an da zasu sanya ido a zaɓen yadda ya kamata. Yayin da muke fatan samun haɗin kan ku, muna tabbatar muku da matukar girmama wa."

Yaushe APC zata gudanar da babban taron ƙasa?

Har yanzun APC ba ta ce komai ba game da sabuwar ranar babban taron ta na ƙasa, amma wata majiya ta ce jam'iyyar na duba yuwuwar yin taron a Maris.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kawunan gwamnonin PDP sun rabu kan tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnonin Kudu da suka fi yawa sun matsa kaimi kan dole sai yankinsu, yayin da na Arewa suka ce ba zata saɓu ba.

Majiya a cikin jam'iyyar PDP ta shaida wa wakilin mu cewa gwamnonin kudu sun matsa kan matakin da kungiyarsu ta gwamnonin Kudu ta ɗauka cewa wajibi mulkin Najeriya ya koma hannun ɗan kudu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262