2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

  • Sanata Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya sanar da cewa ya shirya kazamin artabu idan akwai bukatar hakan
  • A ziyarar da Tinubu ya kaiwa masu martaba a Oyo, ya sanar da cewa babu wata barazana da za ta hana shi cimma burinsa
  • Ya ce ya kai ziyarar ne ga iyayen gargajiyan domin su saka masa albarka, su bashi hadin kai kuma su yi masa addu'ar hayewa shugabancin kasa

Dan takarar shugabancin kasa karkashin All Progressives Congress, APC, Sanata Bola Tinubu, a ranar Lahadi ya sha alwashin cewa babu wata razanarwa ko barazana da za ta dakile masa burin zama shugaban kasa.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da kuma zababben Olubadan, Oba Lekan Balogun.

A watan Janairu Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana shirinsa na fitowa takara a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu ga matasa: Da sannu za ku jagoranci kasar nan, amma sai bayan na ɗana

2023: Na shirya buga wasan yadda ya dace, babu wani abinda zai razana ni, Tinubu
2023: Na shirya buga wasan yadda ya dace, babu wani abinda zai razana ni, Tinubu. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

A yayin jawabi a fadar zababben Olubadan da ke Ibadan, jigon jam'iyya mai mulkin ya ce babu irin barazanar da za ta hana shi cika burinsa.

Ya ce ziyarar da ya kai Oyo da Ibadan duk yayi ta ne domin mutunta kujerun sarautar kuma ya nemi albarka, hadin kai da addu'o'in samun shugabantar kasar nan.

Na shirya kazamin artabu da kowa, Tinubu

Ya ce: "Babu irin razanarwa da za ta iya hana ni. Na shirya duk wani kazamin fada. Na fito ne in zama shugaban kasar Najeriya. Muna dab da tsallakewa."
A yayin jawabi a fadar Alaafin, ya ce: "Ba zan iya fara irin wannan aikin ba ban nemi addu'o'i da hadin kan sarakunan gargajiya ba.
"Na zo nan ne saboda in sanar da iyayena hukuncina na neman kujerar shugabancin kasata. Abinda na ke bukata daga iyayena masu daraja shi ne addu'o'i da hadin kai."

Kara karanta wannan

Magabatan Yarabawa za su ba ka nasarar zama shugaban kasa, Alaafin ga Tinubu

“A yau, da izinin Ubangiji ga ni a kasar Yarabawa ba kamar a baya ba da muke da mataimakin shugaban kasa, ministan ayyuka, cikin gida da wasanni, muna bukatar kari."

A yayin martani, Oba Adeyemi, wanda yayi kira ga ruhin kakanninsu, ya ce an amsa bukatarsa.

Ya ce dukkan magabatan kasar Yarabawa za su yi aiki domin ganin nasararsa da kuma amsa addu'o'insa.

Magabatan Yarabawa za su ba ka nasarar zama shugaban kasa, Alaafin ga Tinubu

A wani labari na daban, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi a ranar Lahadi, ya ce ya na da tabbacin cewa magabatan Yarabawa za su bai wa jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

Daily Trust ta ruwaitoo cewa, Sanata Tinubu ya ziyarci basaraken mai daraja ta farko na kasar Yarabawa a fadarsa da ke Oyo a ranar Lahadi.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, su biyun sun shige ganawar sirri bayan da tsohon gwamnan jihar Legas din ya isa fadar babban basaraken.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa APC Ta Sha Kaye a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Abuja, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Dauda

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng